Labarai

Shugaba Buhari Ya Umarci Sauya Jami’an ‘Yan Sandan Jihar Zamfara.

Advertisment


A kokarin tabbatar da zaman lafiya a jihar Zamfara, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci sauya jami’an yan sandan dake jihar Zamfara domin dakile ayyukan ta’addancin da barayin shanu ke haddasawa.

Shugaba Buhari ya fadi hakan ne jiya a fadar mulki ta Aso Rock dake birnin tarayya Abuja yayin da yake ganawa da tawagar ‘Supreme Council for Sharia in Nigeria’. Shugaban ya kara da cewar, yana iyakar kokarin sa wajen ganin ya shawo kan matsalolin tsaron jihar Zamfara da sauran sassan kasarnan. 

Buhari ya cigaba da cewar, sakamakon rashin gamsuwa da kokarin jami’an yan sanda a jihar Zamfara, ya yi umurnin sauya manyan jami’an yan sanda na jihar da kuma kananan yan sandan da suka kai shekaru uku suna aiki a jihar.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button