Sports

Magoya Bayan Club Din Chelsea Suna Son kungiyar ta Sayo Ahmed Musa

Advertisment

Magoya bayan Chelsea da suka kalli wasan da Najeriya ta lallasa kasar Iceland daci 2-0 ta hannun dan wasa Ahmad Musa sun bayyana burinsu na ganin kungiyar ta siyi dan wasan daga kungiyarsa ta Leceister City.

Magoya bayan kungiyar sun bayyana hakane a shafukansu na sada zumunta na tiwita inda suka dinga yabon dan wasan suna bayyana cewa kungiyar ta siyar da Morata ta siyo Musa domin zai taimakawa kungiyar sosai.

Ahmad Musa dai wanda a yanzu haka yake zaman aro a kungiyar kwallon kafa CSKA Moscow daga kungiyar Leceister City ya zura kwallayen ne a wasa na biyu da kasar Najeriya ta fafata a gasar cin kofin duniya.

Duk da cewa dan wasan yakasa buga abin azo agani a kungiyar ta Leceister City bayan kudin da ta kashe fam miliyan 15 wajen siyansa daga kungiyar CSKA Moscow din a shekara ta 2016 amma mai koyar da tawagar yan wasan Super Eagles ta Najeriya yafara buga wasan dashi a wasan da aka fafata a ranar Juma’a.

Advertisment

Musa dai yayi amfani da kwarewa da gogewa a kwallayen daya zura a wasan musamman a kwallon farko da yayi amfani da kwarewa yayinda kwallo ta biyu kuma yayi amfani da gudu da koma iya wuce yan kwallo.

Ya taba bugawa kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars da kuma BBB Benlo dake kasar Holland sannan kuma ya taba buga gasar ta cin kofin duniya a shekara ta 2014 inda anan ma ya zura kwallaye biyu a wasan Najeriya da kasar Argentina.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button