Sama Da Nera Milyan Dari Da Rarara Yayi Sama Da Fadi Dasu Ashe Filin Kwallo Yaje Yana Ginawa A Kauyen Kahutu
Bayan fara gudanar da bincike ana zargin kudaden da Dauda Kahutu Rarara yayi sama da fadi dasu sama da nera milyan Dari na kungiyar mawaka kauyen su Kahutu yaje yana gina filin kwallo na zamani.
Kafin lokacin Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC ta basu nera milyan 15 su bude ofishi wanda kudaden suka fada akawunt din Dauda Rarara, sai dai kawai ya kira mu yace mana ya kama ofis a (Gwamna Road) dake jihar Kaduna kuma kudaden ma duka sun kare, haka ya kama ofis din babu sanin shugaban kungiyar da matemakin sa da kuma membobin kungiya; inji Yala
Bayan an bude ofishin kungiyar, kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC ta hannun Gwamnan Jihar Zamfara AbdulAziz Yari su suka bayar da kudade a matsayin tallafi, kuma Aminin Dauda Rarara Isyaku Oris ya tabbatar mun an baiwa Rarara nera milyan 100 yanzu haka suna akawunt din sa;inji Ibrahim Yala matemakin shugaban kungiyar
Da Dauda Rarara da Baban Chinedu da Isyaku Oris su suka fara tafiya maganar kudaden amma da za’a koma bai koma dasu ba.
Ibrahim Yala yace yanzu haka idan muka kira Rarara a waya baya dauka a kan maganar kudaden a saboda haka nayi shawarar saka Yanjaridu a cikin maganar ‘Tunda farko nina kwana da sanin cewar Dauda ba tsakanin da Allah yake so a bude wannan kungiyar ba, yana so ne yayi amfani damu kawai’.
Saboda kin yarda daya yi azo a zauna kan kudin shi yasa aka fara zargin da kudaden yaje yana gina (Stadium) a kauyen su Kahutu dake jihar Katsina.
Sources :JARIDAR DIMOKURADIYYA