Jaruma Rahama Sadau Ta Yi Wa Masu Sha’war Yin Fim Nasiha Mai ratsa zuciya
Fitacciyar jarumar nan mai shirya fina-finan Hausa kuma gwanar rawa a masana’antar Rahama Sadau ta shawarci dukkan masu sha’awar bin sahun ta wajen yin fim musamman ma mata da su sa jajircewa a sana’ar ta su.
Fitacciyar jarumar dai ta bayyana hakan ne yayin da take fira da kamfanin dillacin labarai na Najeriya a wani lokaci a baya a garin Abuja, babban birnin tarayya.
Jarumar ta bayyana cewa ga dukkan masu so suyi fice a sana’ar fim din ya zama dole gare su da su jajirce su kuma dage domin cimma burin su.
Da take tsokaci game da irin kalubalen da take fuskanta, jarumar ta bayyana cewa dukkan mai rai daman dole ne ya fuskanci kalubale a rayuwar sa.
Daga karshe kuma jarumar ta sha alwashin cigaba da shirya kayatattun fina-finai domin nishadantar da dumbin masoyan ta a ciki da wajen Najeriya.