Kannywood

HAUWA MAINA: Mutunci Ya Fi Kudi – Irin Mutunci Da Margayyiya Tayi A Rayuwarta

Ashafa Murnai Barkiya

Na fara sanin Hauwa Maina tun cikin shekara ta 2000 ko kuma 2001. Tafiya ce ta hada ni da ita, Ibrahim Mandawari, Shehu Hassan Kano, Hindatu Bashir har da marigayiya Balaraba Mohammed da wasu da na manta, zuwa Gombe. An karrama mu sosai a wannan tafiyar, domin har ganawa mu ka yi da mataimakin gwamnan jihar na lokacin.

Ban sake haduwa da Hauwa ba, sai da wata tafiya ta sake hada ni da ita da wasu zuwa Lagos, a karkashin gayyatar Daraktan Bincike da Tattara Bayanai na Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, a cikin Janairu, 2011. A can ma an karrama mu, domin har ganawa mu ka yi da Jonathan.

Ranar wata Juma’a a cikin watan Janairu, 2011, na fara yin ribas da mota kenan, sai na ji karar shigowar kira a waya ta. Saboda ina gaggawar fita, ban dauka ba, kuma sai aka kara kira dai. Da na duba sai na ga ashe daya daga cikin makusantan Shugaban Kasa na lokacin, Goodluck Jonathan, mai suna Oronto Douglas ne ke kira na.

Oranto Douglas a lokacin shi ne Daraktan Bincike da Tattara Bayanai a ofishin Shugaban Kasa.

Har an bude min kofar fita daga cikin harabar ofis, sai na ce a rufe. Na yi tsaye wuri daya a cikin mota na kira shi. Farkon abin da ya ce min shi ne “Aboki na Ashafa ka na ina?” Na ce masa ina Abuja. Ya ce min ya tambayi wani domin a hada shi da wanda ya san ‘yan fim din Hausa, sai aka ce masa ya sa a nemo masa wani mai suna ‘Ashafa’, wanda shi ne editan LEADERSHIP HAUSA. Shi kuma Doughlas sai ya ce musu ai ya san ni, wai ni abokin sa ne ma sosai domin mu na hulda tare. To a gaban su ne ma ya kira ni nan take domin su tabbatar.

Maganar gaskiya na yi kusanci sosai da Douglas musamman irin yadda ya rika nuna sha’awar ganin ana yayata ayyukan da ubangidan sa, Goodluck Jonathan ya rika yi ana bugawa a kafafen yada labarai na Hausa, wadanda ba na gwamnati ba. Kusanci na da shi ya karu saboda sau da yawa ya na sa ni aikin da aka rigaya aka sa wasu su yi, amma ba su abin yadda ya kamata ba. Ko kiran da ya yi min a ranar ma ya yi ne saboda wani aiki da ya ke so mu yi, wanda aka ba wasu su yi, amma su ka nuna son kan su. Wannan aiki kuwa shi ne sanadin mutunci na da Hauwa Maina.

Oronto Dauglas ya ce min ya na so na ba shi sunayen ‘yan fim na Hausa da za a gayyata wani taro a Lagos, amma kuma ni ma na tabbatar na halarci taron. Na ba shi sunayen ‘yan fim maza da mata ina tunanin sun kai goma ko sha biyu.

Cikin wadanda na bada sunayen su har da marigayiya Hauwa Maina. Kafin na ba da sunan ta kuwa, na kai shekara goma ban gan ta ba, ita ma ba ta gan ni ba. Na bada sunan ta ne, don na san da irin zurfin ilmin ta za ta iya yin bajintar da ba za a ga wallen ‘yan fim din Hausa a Legas ba, ballantana a raina Hausawa.

Bayan mun dawo taron da kwana uku kuma sai Oronto Douglas ya sake kira na. Ya ce min ya so na samo ‘yan fim mata guda biyu daga Kannywood, amma wadanda suka iya Turanci sosai, don a hada su da wasu ‘yan fim mata na Nollywood domin a ba su wata talla, a Lagos. Ya ce min amma aikin na gaggawa ne, ya na so su tabbatar a yau sun bar duk inda su ke sun iso Abuja. Kuma ya ce ya ba ni minti 30, zai sake kira na. Na ce masa an gama.

Ina gama waya da shi, sai na kira Hauwa Maina na shaida mata. Kuma na ce mata duk abin da ta ke yi, kada ta kara awa biyu a Kaduna, ta shirya kawai ta nufo Abuja. Baya ga Hauwa, na kuma kira wata jarumar guda daya, wadda dama da ita aka je taron Lagos. Ita kafin haka, ban ma taba ganin ta ba sai a hoto ko a cikin finafinai, amma ita ma din na san ba za ta bayar da Hausawa ba. A yanzu ta na gidan mijin ta.

Bayan sun tabbatar min da cewa duk su na Abuja kuma har an ba su masauki tare da wasu daban, ban sake komawa ta kan su ba, tunda dai na san na cika wa Douglas bukatar sa ta neman wadanda su ka iya Turanci sosai. Da dare ya kira ni ya yi godiya, ya ce min ya bai wa masu shirya tallar lambobin su, amma shi ko ganin su ma bai yi ba.

Bayan kwana hudu da safiyar wata Lahadi, ina tsaye bakin wani banki da nufin yin amfani da katin ATM na cire sauran canjin da ke cikin asusu na, sai na ga Hauwa Maina ta kira waya ta. Ba gaisuwa, ba komai a cikin gaggawa sai ta ce min, “Oga Ashafa ka na ina?” Na ce ina Abuja. Ta ce min, “to don Allah ga nu nan an sauke mu Hilton Hotel, za a zo nan da minti 20 a dauke mu zuwa airport a maida mu Lagos. Don Allah ka yi sauri ka zo, mu na son ganin ka kafin mu fita.”

Nan take na bar wa mai gadin banki sallahun ajiyar mota ta, na yi sauri na hau motar haya, gudun kada na shiga harabar otal din na rasa wurin ajiye mota da wuri. Kafin na karasa kuwa Hauwa ta kira ni ya kai sau biyar, ina ce mata ga ni nan na kusa isa.

Ina shiga inda su ke ita da daya jarumar, sai na same su kowace na ta gaganiyar zuba kaya a cikin jaka. Su ka ce min ga kudi nan a cikin leda kusa da inda na zauna, sun ba ni ne godiyar mutuncin da na yi musu. Su ka rika sheka min ruwan godiya a lokaci daya kuma su na cusa tarkacen kayan kwalliya cikin jaka.

Bayan na fito na sake shiga taksi, na nufi bakin bankin da na ajiye mota ta da nufin cirar sauran ‘yan canji. Canjin da ban cira ba kenan a ranar. Da na duba kudin da su ka ba ni, sai na ga kudi naira milyan daya cif da cif, kuma dukkan su ‘yan naira 200 ce sabbi dal kunshe dandir-bandir. Kowace ta ba ni rabin milyan kenan.

Bayan sati daya kuma sai suka neme ni, suka ce min ga wata talla su kuma sun samo, amma da Hausa ake so a yi tallolin, kuma ba su ma san yaya za su yi ba. Amma duk da haka su ka ce ai za su iya, sai aka ba su. Muka zauna da su duk na tsara yadda za a yi tallar. A lokacin na dauka tsara musu kawai su ke so na yi.

Bayan na kammala, sai suka bude jaka, suka rungumo kudi suka ba ni. Su ka ce ka je kai ka san wuraren da za ka bayar da tallar, kuma kai ka san abin da za ka iya samu a ciki. Na ce musu ku kuma fa? Su ka ce min ai sun cire na su, wai mamakin yadda na tsara tallar su ke yi a cikin kankanin lokaci haka. Kafin sannan kuwa, daga Lagos zuwa Abuja, su na ta tunanin yadda za a yi tallar.

Tun daga wannan ranar ban kara ganin Hauwa Maina ba, sai cikin 2017, amma mu na yin waya mu na gaisawa. A duk lokacin da muka gaisa za ta ce min, “Don Allah Oga Ashafa a rika haduwa ana gaisawa. Ai mutunci ya fi kudi. Idan wata sabga ta tashi a gidan ka, ka rika sanar da ni mana. Ai mutunci ya fi kudi, Abin da ka yi min ba zan taba mantawa ba, amma ka sani idan zumunci ya dore, to fa ba za a manta baya ba.

Na kan nuna wa Hauwa Maina cewa ta fahimci ni da ita kowa harkokin gaban sa sun sha masa kai. Ni ina Abuja, ita kuma ta na Kaduna, sannan ni kuma ba shiga sha’anin ‘yan fim na ke yi a yanzu ba, ballanatana mu rika haduwa a wasu taruka.

Daga baya sai na rika jin maganganu a Kaduna, sannan ita ma ta rika kira na a waya ta na shaida min cewa ta sha tsangwama saboda siyasa don sun yi tallolin zaben wanda masu tsangwamar ta ba su so.

To a nan ina da tambaya. Don me za a tsangwami dan talla? Ta ce dole sai ka zabi wanda ta tallata ne?  Wannan wane irin gidoganci ne? Ita ma talla aka ba ta. Duk duniya akwai wannan ka’idar ta talla ga jaridu
, gidajen radiyo, talbijin, mujallu da ‘yan wasa da aka fi sani da ‘celebrities.’ Kai da ka tallata na ka wa ya tsangwame ka?

To yanzu dai kama daga wadanda suka rika jin haushin ta zuwa wadanda suka rika yi mata barazana, Hauwa ta tafi ta bar muku duniyar. Ku kuma sai ku fadada gidajen ku domin ku kara baza shimfidun da za ku ci gaba da yi wa duniya zaman-dirshan, zaman dimum-da’iman, daga nan har bisa Mahdi.

Ban sake haduwa da Hauwa Maina ba, sai a cikin 2017, a tashar jirgin kasa ta Kubwa, Abuja. Mu ka kuwa yi sa’a kowanen mu ya isa da jijjifin safiya, kafin lokacin shiga jirgi. Ta rika ba ni labarin irin halin da ta ke ciki dangane da auren ‘yar ta da ya gabato a lokacin. Ta ce min dalilin batun auren ne ta zo Abuja har muka hadu a filin jirgin kasa kan hanyar komawar ta Kaduna.

Maganar gaskiya na jinjina wa Hauwa jin yadda ta rika ba ni labarin irin hanyar da ta tarbiyantar da ’yar ta Maryam, da za ta yi wa aure. Na ga kokarin ta matuka jin yadda ta sha gaganiyar kashe makudan kudade wajen ilmantar da yarinyar har zuwa kammala jami’a.

Irin yadda ta ke dora tawakkali ga Allah a kan dukkan al’amurra na rayuwa, na fahimci hakan ya kara mata kwarin guiwa sosai wajen kaiwa ga wasu nasarori da ta samu da kuma fuskantar wasu kalubale na rayuwa.

Ban san Hauwa ta kwanta jiyya asibiti ba, sai labarin rasuwar ta kawai na ji. Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un.

Kamar yadda ta sha ce min ba za ta taba mantawa da mutuncin da na yi mata ba, ni ma ba zan taba mantawa da mutuncin da ta yi min ba.

Hauwa Maina. Ina ganin mutuncin ki. Allah ya azurta bayan da ki ka bari. Allah ya bai wa iyalan ki juriyar hakurin rashin ki. Allah ya gafarta miki. Allah ya sa mutuwa hutu ce.

*ASHAFA ya yi aiki da mujallar FIM, LEADERSHIP HAUSA, RARIYA, yanzu kuma ma’aikaci ne a PREMIUM TIMES, Abuja.
[email protected]
08056363602
9 Ga Mayu, 2018.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button