Kannywood

Mawaki Daya Yafi mayaka Dubu A Fagen Gaba – Inji Nura M Inuwa

Babban mawaki nura m inuwa ya yayi wannan sharhi ne a shafinsa na instagram idan yake cewa.

Bansan me zance game da mawaka ba Amma dai na kasa gane ina tunanin mu yayi da muka kasa gane matsayin mu ga al umma. Inaso mu tuna mu ake kawowa tallan baki mu cewa jama a fari ne, a kawo mana na mummuna muce kyakykyawa ne jama a su karba, kunga ashe muma jagorori ne ababan duba ga jama a, da wannnan nake son jan hankalin mu da mu tsaya mu taimaki kawunan mu, mu taimakin yan uwan mu, jama a sunada damuwoyi amma basu da muryar fada aji, mu kuma  da ALLAH ya bamu sai mukafi son kawunan mu,maimakon mu fadi gaskiya mu zauna da mutunci, sai muka zabi mu fadi karya a dan bamu abin da bazai rabamu da talauci ba,kaico tirr da wannan dabia ar tamu,matsayin mawaki daya yafi na mayaka dubu a inda akaci gaba,mu tsaya ga ALLAH  mu zama karnikan farauta ba.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button