Abubuwan Da Ya Dace Shugaba Buhari Yayi A Masana’antar kannywood – Inji Darakta Kamal S Alkali
Fitaccen daraktan fina-finan Hausa, Kamal Sani Alkali ya ce abubuwan da yake so Buhari ya yi wa masu shirya fina-finan Hausa na Kannywood su ne, ya sanya gwamnatin tarayya ta samar da tsare-tsare na musamman da za su sanya masana’antar ta rika samun ci gaba mai dorewa.
Daraktan, wanda shi ne shugaban Kamfanin Kamal International Limited mai babban ofishinsa a Kano ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilin Aminiya ta wayar tarho.
Alkali wanda ya bada umarni a manyan fina-finai da suka hada da ‘Umar Sanda’ da ‘Sahabi’ da kuma ‘Guguwar So’ ya ce, rashin isasshen jari a wurin ’yan fim da karanci sinimomi da kuma matsalar satar fasaha ne suka hana Kannywood bunkasar a-zo-a-gani, inda a yanzu masana’antar take cikin wani hali.
Ya ce, “Ina so gwamnatin Buhari ta gina manyan sinimomi a Arewacin kasar nan, sannan ta ba ’yan fim bashin da babu kudin ruwa a cikinsa, ko tallafa wa ’yan fim da jari, ko dai ta ba su bashin da babu kudin ruwa a cikinsa don su gina sinimomin a Arewa.
“Idan gwamnatin Buhari ta yi hakan, to Kannywood za ta bunkasa, bunkasar da za ta sa ta rika gogayya da manya-manyan masana’antun fina-finai na duniya,” inji Kamal.
Daraktan wanda ya lashe Gwarzon Darakta yayin Gasar City People Entertainment ta 2017 ya kuma bukaci gwamnatin Buhari ta samar da ingantacciyar hanyar yaki da masu satar fasaha ko barayin zaune da suka addabi masana’antar fiye da shekara 15.
Ya ce, “Kannywood tana cikin ta mawuyacin hali, zan iya cewa ta kusa durkushewa saboda masu satar fasaha da barayin zaune. Kada a manta kafin kowane fim ya fita sai an biya Hukamar Kare Hakkin Mallaka ta kasa Naira dubu 15, sannan a biya Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano Naira dubu 10 da dari 500, amma hukumomi sun kasa samar da nagartacciyar hanyar yaki da masu satar fasaha.”
Alkali wanda ya tsara labaran fina-finai irinsu, ‘Jarumin Maza’ da ‘Gaba Da Gabanta’ ya kuma shawarci gwamnatin tarayya da ta zuba jari a masana’antar don ganin an samar da fina-finai masu inganci.