Ta Leko Ta Kuma : Wata Tsohuwa Ta Damfari Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
A kwanakin baya hadiman shugaban kasa Muhammadu Buhari sun wallafa a kafafen sadarwa na zamani cewa, matar Marthin Luther King Jr sun karrama shi da kyauta mafi daraja da aka taba ba wa wani bakar fata a Afirka.
Sai dai daga baya Cibiyar The King Center, wacce ke adana tarihin fitaccen bakar fatar nan na Amurka, marigayi Martin Luther, ta nesanta kanta daga lambar yabon da aka bai wa Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya.
Martin Luther King Jr. Ba’amurke ne kuma bakar fata, babban jagoran addinin Kiristanci, dan gwagwarmayar kwatar ‘yanci, wanda ya shahara a duniya a matsayin gwanin iya sarrafa harshe, kana kuma ya zama jagoran fafutukar kwatar ‘yanci daga 1954 zuwa 1968.
Coretta Scott King marubuciya ce kuma Ba’amurkiya, jagorar kungiyar gwagwarmayar kwatar ‘yanci kana kuma matar Martin Luther King, Jr. Coretta Scott King ta taimaka wajen gwagwarmaya a shekarar 1960.