Muhimman Abubuwa Tara (9) Da Suke Kare Yaro Daga Fadawa Halaka Idan An Gina Shi Akai – Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
TUN RAN GINI TUN RAN ZANE
MANZON ALLAH SAW YACE : DUK ABIN HAIHUWA, ANA HAIHUWARSA AKAN FIDRA TA ADDINI, IYAYE SU KE YAHUDANTAR DA SHI, KO SU NASARANTAR DA SHI, KO SU MAGUZANTAR DA SHI.
BUKHARI DA MUSLUM.
IDAN KAGA YARO DA AL’ADUN YAHUDAWA, KO MAGUZAWA KO NASARA.
daga irin tarbiyyar ce gurbattaciya da ya samu daga mahaifansa, ko daga sakacin mahaifansa.
1. na daya, imani da ingattaciyar akida
2. na biyu Ibada ga Allah Kamar sallah azumi tun yana yaro.
3. Na ukku halaye na Kwarai kamar gaskiya da kunya da amana da mutunci.
4. na Hudu: Ilmi na addini da zamani.
5. Na biyar : kula da lafiya da nisantar kayan maye.
6. Na Shida : zamantakewa Girmama Manya Da Tausayawa Kanana, da a bawa dukkan mai hakki, hakkinsa.
7. Na Bakwai: Koya Masa sana’a Da Aikin yi. Domin Ya Dogara Da Kansa.
8.Na Takwas: Nuna Masa Illar Zina Da Luwadi Da madigo, Sa Dukkan mu’amala Mai Muni.
9. Na Tara: Addua, Ta Neman Kariya Da Tsari Daga farmaki Shedan.
Allah Ka Bamu Yaya Masu Albarka Da Tarbiyya.