Labarai

Mai Bada Shaida A Shari’ar Maryam Sanda, Yayi Layar Zana A Kotu.


Mai gabatar da shaida a shari’ar da ake yi wa Maryam Sanda, wacce ake zargi da laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello, ya sulale daga kotu a yau Litinin tun kafin mai shari’a ya kira shi ya bada shaida.

Mai gabatar da shaidar mai suna Alhassan Abdulmumin, ya isa kotun tare da tawagar masu gabatar da kara domin ya bayar da shaida amma lokacin da aka shiga kotu, alkali ya nemi ya zo ya bada shaida, sai aka rasa inda ya ke.

Maryam dai ana tuhumar ta ne tare da mahaifiyar ta da kuma wani dan uwan ta, amma duk an bada belin su.

Lauya mai gabatar da kara, James Idachaba, ya bayyana wa mai shari’a cewa watakila Alhassan ya sulale ne saboda ya na tsammanin ba za a saurari bayanin sa ba ne saboda abin da ya faru a kotun a ranar Litin da ta gabata.

An dai rigaya an bada belin Maryam a bisa sharudda masu tsauri, ciki kuwa har da rubutacciyar yarjejeniya da mahaifinta cewa zai rika gabatar da ita a duk ranar da za a yi zaman shari’a.
Alkali Yusuf Halilu ya daga karar sai ranar 19 Ga Afrilu, 2017, nan da wata daya kenan daidai.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button