Kannywood

Ki Rungumi Tsarin Musulunci Zaki Zauna Lafiya A Gidan Miji – Martanin Datti Assalafy Ga Fati MuhammadTsohuwar guzuma kuma tsuhuwar ‘yar wasan kwaikwayo Fati Muhammad kwanaki ta rubuta a shafinta na facebook cewa; ”Ban taba ganin mazan da suka mayar da mace marar ‘yanci ba kamar mazan hausawa”.

Kwanaki can baya haka naga bayin Allah a wannan dandali na facebook suka ruwaito kalaman da ita wannan tsuhuwar guzuma ta furta akanmu mazan hausawa inda tace; ”Mazan hausawa auren sha’awa sukeyi musu, da zaran sun aure mace sun kashe wutar sha’awarsu da ita sai su sake ta, shiyasa ita Fati Muhammad ta kasa zama a gidan miji a cewarta”.

Zan wakilci ‘yan uwana Hausawa, a gaskiya Fati Muhammad sharri kika mana, mu Hausawa babu wanda ya kaimu iya rikon matanmu na aure, korafin da kikayi cewa ana muku auren sha’awa to ai ku ‘yan wasan kwaikwayo kuka jawa kanku ake muku auren sha’awa, tunda kayan sha’awa dake jikinku wanda Allah (T) yace ku rufe ku boye kuke tallatawa da sunan wasan kwaikwayo.

Shiyasa ‘yan nanaye da ‘yan daudu zasu ganku suyi sha’awar abinda kuka tallata musu su nemeku ta aure ko fasadi suna kashe wutar sha’awarsu sai suyi watsi daku daga baya, kamar yadda wasu manyan attajirai da ‘yan siyasa suke kwana daku a hotel suna baku makudan kudaden al’umma da suka sace.

Mafita gareku shine kuyi watsi da sana’ar wasan kwaikwayo ku dena tallata kayanku na sha’awa, ku koma makarantar addini a baku tarbiyya islamiyya, Hausawa ustazan kwarai zasu aureku su rikeku amana da hakuri da tausayawa.

Allah ya shiryeku damu gaba daya, ya tabbatar damu a tafarkin gaskiya.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button