Kannywood
kalli Hotunan Manyan Jarumai Sun Halarci Happy Birthday Taya Murna Zagoyowar Ranar Haihuwar Nafisat Abdullahi
Manyan masu ruwa da tsaki a harkar fina-finai hausa na masana’antar Kannywood sun halarci walimar taya murnar zagoyawar ranar haihuwar jaruma Nafisa Abdullahi.
A ranar laraba 24 ga watan janairu ne jarumar ta cika shekara 27 a duniya.
Domin nuna farin cikin zagoyowar wannan muhimmin ranar a rayuwar ta ta hada wata walima ta musamman wanda har ta gayyaci kawaye da abokan huldar ta a masana’antar kannywood.
Anyi wannan sharholiyar a dakin cin habinci na bristol palace hotel dake Kano.
Manya baki da suka halarci wajen walimar sun hada da shugaban hukumar tace fina-finai na jihar kano Alhaji Ismail Na’abba Afakallah da masu shirya fina-finai Aminu Saira da Nazir Dan hajiya.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com