Kannywood

Dawo Da Rahama Sadau Harkar Fim; Akwai Sauran Rina A Cikin Kaba



 Rahama Sadau ta dawo Nigeria bayan tayi wata biyu a kasar Cyprus

Rahama Sadau ta sauka a Nijeriya a ranar 21 ga January bayan ta shafe watanni biyu da rabi ta na karatu a kasar Cyprus.
Fitacciyar jarumar ta sauka ne  da safe a Abuja, babban birnin tarayyar kasar.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa babu wani dan wasan fim da ya kai Rahama Sadau jan hankali a kafafen watsa labarai a cikin shekarar 2017.

Hakan ya faru ne saboda ce-ce-ku-cen da aka sha yi a kan korar ta daga masana’antar fim ta Kannywood da kungiyar masu shirya finafinan Hausa ta MOPPAN ta yi a cikin Oktoba, 2016.

Korar ta biyo bayan rawar da jarumar ta yi da mawakin hip-hop mai suna Classiq a bidiyon wakar sa ta “I Love You” inda su ka yi rungume-rungume.

Kungiyar ta ce bullar bidiyon wakar ya kara jawo wa masana’antar tsangwama a wajen jama’a, musamman masu cewa ‘yan fim na bata tarbiyya.

Bayan shekara daya da korar tata, Rahama Sadau ta rubuta wa kungiyar wasika inda ta bada hakuri kan abin da ta aikata, tare da bada tabbacin cewa hakan ba zai kara faruwa ba.

A watan Nuwamba da ya gabata, kungiyar ta gayyato jarumar zuwa wani taro inda za su tattauna kan batun d’age mata takunkumin, to amma sai jarumar ta sanar da su cewa ita yanzu ba ta kasar, ta na Cyprus, kuma ba za ta dawo ba sai a farkon Fabrairu na 2018.

Hakan bai yi wa shugabannin kungiyar dadi ba saboda jarumar ba ta sanar da su cewa ta yi tafiya ba.

Da yawa daga cikin shugabannin kungiyar sun kalli abin da ta yi a matsayin “rainin wato” ga kungiyar.

Saboda haka su ka kauda duk wata magana ta yafe mata har sai ta dawo Nijeriya ta sake neman zama da su.

To amma a watan jiya sai Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta bada sanarwar cewa ita ta yafe wa Rahama, kuma za ta duba duk wani fim da ta shirya ko ta fito a ciki.

Shugaban hukumar, Malam Isma’il Na’abba (Afakallahu) ya fada wa mujallar Fim a wata hira cewa hukumar sa ta yafe wa jarumar ne saboda ai ko Allah ma ana yi masa laifi Ya yafe, kuma ba za a dinga zama a haka ba tare da an yafe mata ba.

Furucin nasa bai yi wa MOPPAN dadi ba, har ta ce wannan karya alkawari ne Afakallahu ya yi.

Sakataren kungiyar, Malam Salisu Mohammed (Officer), ya ce hukumar ba ta da hurumin yafe wa Rahama, kuma ai hukumar ta amince da kudirin kungiyar na cewar sai kungiyar ce kadai za ta iya dawo da jarumar.

Officer ya tabbatar wa da mujallar Fim cewa kungiyar za ta maka hukumar a kotu idan har ta tsaya a kan cewar ta d’age wa Rahama takunkumin.

Shi ma shugaban kungiyar MOPPAN na Jihar Kano, Alhaji Kabiru Maikaba, ya bayyana cewa hukumar ba ta da hurumin yafe wa Rahama domin ai ba ita ce ta kore ta daga industiri ba.

Ya ce su a wurin su har yanzu Rahama korarriya ce, kuma ba su amince da yafewar da Afakallahu ya yi mata ba.

Maikaba ya nanata cewa kungiyar sa za ta dauki kwakkwaran mataki a kan batun cewar wai hukumar ta yafe wa jarumar bayan su MOPPAN ba su yafe mata ba.

Ya ce za su zauna tare da hukumar domin samun matsaya a kan lamarin.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa ita dai Rahama Sadau ta nemi yafiya ne saboda ta samu damar fitar da sabon fim din ta mai suna ‘Dan’iya’ sannan ta fi gaba da fitowa a finafinan Hausa.
Yanzu haka ta sa ranar fara nuna shi a gidan sinima na Film House da ke Kano a watan gobe.

Mutane sun sa ido su ga yadda MOPPAN za ta hana nuna fim din tare da fitar sa a kasuwa bayan Hukumar Tace Finafinai ta bada izinin hakan.
©Zuma Times Hausa

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button