Yadda Anka Kaddamar Da Taron Gabatar Da Fim Din Sarauniya
Daga Wakilinmu, Kano
Kamfanin shirya finafinai na Rite Time Multimedia ya shirya wani taron biki na gabatar a fim din Sarauniya da ya kammala aikin wanda a ke sa ran na gaba kadan za a shigar da shi kasuwa.
Taron wanda a ka gudanar a ranar Asabar 25 ga watan Nuwamba a babban dakin taro na otel din Ni’ima da ke cikin garin Kano, an fara shi ne da misalign karfe 8 na dare. Tun da farko da yake jawabi a game da wanan aro, Muhammad Mujahid ya bayyana manufar taron ne da nufin za a haska wani bangare na wannan fim ne Sarauniya domin jama’a su gani daga wani bangare da fim din ya kunsa, sannan kuma za a bayar da kyautittika na karamawa ga jaruman da suka bada gudunmuwa a cikin wannan fim din.
Don haka a ka gayyato manyan mutane su gani don su san irin aikin da wannan kamfni na Rite Time yake gudanarwa. Domin kuwa kamfani ne da ya dade yana kawo ci gaba a masana’antar mu ta Kannywod wajen shirya finafinai masu inganci da samawa matasa usu da aikin yi. Don haka muna fatan Allah ya sa nasara a wannan taro, Allah ya sa mu yi lafiya mu tashi lafiya.”
Bayan gama jawabi ne sai aka gabatar da ‘yan rawar koroso inda suka dauki lokaci suna nishadantar da taron.