Labarai

Shugaba Buhari Ya ‘Yanta Fursunoni 500 A Kurkukun Kano

A shirin gwamnatin tarayya na rage cunkoson gidajen yari dake fadin kasar nan, shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Laraba ya ‘yanta fursunoni guda dari biyar a gidan yarin Kurmawa dake birnin Kano.

Shugaba Buhari wanda ya je gidan yarin tare da rakiyar gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kuma yi kira ga wadanda aka ‘yanta din da su sauya dabi’un su don ganin sun zama ‘yan kasa nagari.

Idan za a iya tunawa, a kwanakin baya ne shugaban kasan ya bada umarnin a rage yawan jama’ar da suke tare a gidajen yarin kasar nan sakamakon cunkushewa da gidajen yarin kasar nan suka yi.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button