Uncategorized

Masu Kudi Suji Tsoron Allah Su Taimakawa Talakawa karanta kuji Daga Sheikh Jabir Sani Mai Hula

Masu kudi suji tsoron Allah su taimakawa talakawan da ke unguwar su, da ‘yan uwan su, da makwabtan su. Annabi S.A.W. yana cewa: “Duk wanda ya kwana a koshe makwabcin sa najin yunwa baiyi imani ba.”  Ťabrānī da Hākim suka ruwaito, Thahabī da Albānī suka inganta.
Masu roko suji tsoron Allah su tausayawa masu bayarwa. Idan kaje da bukatar dubu daya kasamu dari biyu kayi hakuri, masu rokon yawa ne dasu. Idan kana zaton mutum yana da milyan goma ka kai masa bukatar dubu goma zaiyiyu ku goma ne kuka je gunsa a wannan ranar. A karbi kadan ayi hakuri.
Ya Allah duk wanda ke cikin tsanani ya Allah kayi masa mafita, duk mai taimako ya Allah ka kara yelwata masa.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.comMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button