Labarai

Ban Umarci Magoya Bayana Su Koma PDP Ba – Kwankwaso


Daga Abubakar Abba
Tsohon Gwaman jihar kuma Sanata mai wakiltar mazabar jihar ta tsakiya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya karyata rahotanni da wasu kafafen yada labarai cewar wai ya umarci magoya bayansa su koma jam’iyyar PDP.

Kwakwaso ya maida martanin ne a kan wata hira da dan’uwansa Musa Ilyasu Kwankwaso ya yi, inda ya ce, Kwankwaso ya umarci magoya bayan
sa su canja sheka zuwa PDP.

A wata sanarwa da mai yada labaransa Binta Spikin ta fitar, kwankwaso ya ce,” rahoton ya kidima ni kwarai, inda ya ce, maganar ta dan’uwan nawa, karaya ce tsagwaronta.”
Acewar Kwankwaso, “a yaushe dan’uwan nawa ya zama kakaki na har da zai zabga wannan karyar a kaina, wannan ba za ta taba sabuwa ba.”

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button