Aure Ibada Ne! Rashin Sa Tawaya Ne – Sheikh Aliyu Said Gamawa
?? Hakika Allah ya aiko mazanni kafin Manzon Allah Annabin mu Muhammad (saw) kuma aka sanya su masu aure masu zuriya.., hakanan a tarihin rayuwar farin jakada Annabi (saw) shima an tabbatar yayi aure kuma yayi zuriya.
?? Yana daga cikin sunnnah mai girman lada yin aure.. An umarci matasa duk wanda ke da damar yin aure to yayi aure, haka nan an umarci iyaye in wanda suka amincewa halin sa da addinin sa yazo neman auren ‘ya ‘yansu su aurar masa.
?? Aure cikar kamala ne, karin daraja ne, akwai falala mai yawa da samun rayuwa mai dadi cikin zaman aure. Hatta nishadin zaman aure lada ne. Rashin yin aure ga mai iko gazawa ce da tawaya, maras aure na rayuwa cikin rauni da kaskanci da matsaloli.
?? Ga duk wanda ya girma tabbas dabi’ar nan ta halitta na son iyali zata bishi har zuci ta qawata masa son aure da burin samun zuriya. Allah ya sanya mana soyayya da tausayi tsakanin maza da matan mu.
?? Rayuwa dace ne, kuma rabo ne, wato ba kowa ne ke samun abinda yafi ba, ko samun abinda yake so a rayuwar sa. Allah sarki tausayin maras aure ya kamani…..
?? Hakika da so samu ne, ina ga duk al’ummar mu maza da mata ba mai za6awa kansa jinkirin aure. Ko ace namiji yana dama da iko da karfin ga66ai da lafiyar kwakwalwa ya zauna da mata daya. Ko mace yar gidan daraja, mai gata da lafiya ta daskare a gida har ta gama girmanta ba aure.
?? Na yarda da masu hasashen cewa jinkirin aure na jawo mana matsoli sun fi shurin masaki ga maza da matan mu a yau. Akwai masu cewa shike jawo yawan samun yasar da jarirai, fyade, fandarewa iyaye, shaye-shayen ‘yan mata, yawon ta zubar da kallon fina-finan batsa da sauran irin su…
?? Muna rokon Allah ya bada ladan jarrabawa ga wadanda wani laruri ya jawo masu jinkirin aure. Allah ya aurar dasu su rayu aminci da natsuwa. Allah ya musanya masu damuwar da suka ji da farin ciki a duniya da lahira.
?? Sauran matasan mu da iyayen da ke zuba ido suna ganin ‘ya ‘yan su maza ko mata suke share gida bisa gan-ganci su zauna cikin gata da sunan jiran kammala dogon karatun boko, da sauran dalilai masu rauni da wassu ke bayarwa na rashi auren su muna rokon Allah ya shiryar dasu ya kwadaitar dasu son samun falala da darajar aure a rayuwar su. Hakika aure daraja ne, samun haifuwa albarka ne..
?? Masu kyamar yin aure don burin buga duniya, da kwadayin sheqe aya, sai muce ga ku ga yau da gobe, karshe dai tabbas afkawa ne cikin ramin nadama da matsaloli iri-iri. Allah ya tsare mu.
?? Tir da masu barin zuciya ta rinjaye su ta hannun haggu, wadannan sune masu mantawa da batun yin aure, da masu watsi da maganar yin aure, da masu shirin auren suna fasawa… in ka ta6a su sai suce da lokaci…
?? Ina masu cewa ai mazan ne… mazan kuwa suce ai matan ne…Irin wadannan a haka suke cinye damar rayuwa da aka masu baiwa da ita, tun ana yayin su, tun suna burge kowa…. har su dawo sai dai ayi maleji dasu…
?? Dubi fa yadda wassu iyayen don sakaci ko zamananci ke barin ‘ya ‘yan su maza ko mata su gawurta a gida, a karshe a zo a cusa su da kyar. Wassu fa kamar ace ana auren su ne bayan expiring..
?? Yanzu ina mafanin a bar yarinya ta girma har ta kai zangon da zata fara mummunan tunanin ita fa ta girma, kuma ta waye, don haka ba wanda zata bari ya sa6awa ra’ayinta, tana da tsare-tsatenta da ba mai keta mata su, ba mai ta6a mata ‘yancin ta na hulda da abokanta maza da mata, tana da irin abincin da ta tafi so, ba mai iya hanata fita yawon ta, wata ma a mota an sa bakin glasa…kai duniyar nan!
?? Tabbas sakacin al’ummar mu na barin koyarwar addini da watsi da kyawawan al’adun mu ne yake jawo mana yawan samari da ‘yan mata ba aure, da yawan bazawarai a kusan kowanni gida….kafin ma auren ma wata dogon zaman da tayi a gida da ‘yancin da uwa da uba suka bata… ya jawo mata matsalolin da zasu hanata zaman aure wato sharuddan sakin ta sun cika..
?? Malamai fa sunyi ta wa’azi da hudubobi har yawun su ya fara bushewa, wassu ma masu wannan jinkirin sun san fari da baki.. tsabar zamanan ci ne. Wassu ko koyi ne da turawa da biyewa zamani….! Allah ka shirayr da mu.
?? In mun yarda wannan matsala ce a yau, to ina mafita?????
Ya Allah ka kawo Mana Agaji Na Gyara a cikin Wannan Al’umma tamu