Addini

SHIGAR DA SU SHEIK BALA LAU SUKE YI A KASASHEN TURAWA SHINE DAIDAI A MAHANGAR ADDIN GA HUJJOJI KAMAE HAKA

Wani bangare na mutane suna suka da aibanta Shugaban Izalar Najeriya da Sakaren sa akan irin tufafin da suke sanyawa a kasashen turawa, imma zargi da sukan nasu ya kasance da kyakkyawan manufa suke yi ko kuma da munmunan manufa, to koma dai yayane ga bayani takaitacce.

Idan mutum ya tafi wani gari ko wata kasa to abinda ake bukata daga gare shi shine ya sanya irin tufafin mutanen garin, bai dace ya saba mu su ba, kai saba musu ma makruhine.
Yazo cikin Mausu’atul Fiqhiyyah a 6/154 cewa:-
لبس الألبسة التي تخالف عادات الناس مكروه لما فيه من شهرة، أي ما يشتهر به عند الناس ويشار إليه بالأصابع، لئلا يكون ذلك سببا إلى حملهم على غيبته، فيشاركهم فى إثم الغيبة.
Sanya suturar da ta sabawa al’adar mutane makruhi ne sbd abinda yake cikin sa na shahara, abin nufi abinda yake yin shahara da shi a wurin mutane har ana yin ishara da yatsu zuwa gare shi, sbd kada hakan ya zama sababi da zai sanya su yin gibar sa, sai shima yayi musharaka da su cikin zunubin giba.

Sheik Uthaymeen a Liqa’ul Babul Maftuh 24/148 (Allah ya jikansa) yace:-
والسنة في كل إنسان أن يلبس ما يلبسه الناس، ما لم يكن محرما بذاته، وإنما قلنا هذا، لأنه لو لبس خلاف ما يعتاده الناس لكان ذلك شهرة.
لقاء الباب المفتوح 24/148.
Abinda yake Sunnah game da kowane mutum shine ya sanya suturar da mutane suke sakawa, matukar bai zama haramun a zatin sa ba, mun fadi hakane sbd da ace zai sanya tufafin da yake sabanin abinda mutane suka rike shi a matsayin al’adar (su wurin sanya tufafi) to da hakan ya zama shuhura.

Ga abinda babban Malamin hadisi kuma Malami a Masallacin Manzon Allah Sheik Al’abbad yace:-
 وإنما الذى لا ينبغي هو أن يكون في بلد ويأتى بلباس غريب.
شرح سنن أبي داود 29/73
Abinda bai dace ba shine mutum yazo da tufafin da yake baqo ne (a wurin mutane tufafin da ba su san da shi ba a wurin su).

Don haka masu sukan su Sheik Bala Lau akan suturar da suke sanyawa a kasashen turawa suna sukan su ne kawai a bisa jahiltan addini da kuma jahiltan rayuwa.

Sbd haka masu sukan su sune jahilai, amma su Sheik Bala Lau sun gina lamarin su ne a bisa shari’ah.

Sanann su masu zagi da suka sun manta yanzu lokacin sanyi ne matuka kuma sanyin da ake yi a wadancan kasashen yafi sanyin da ake yi anan Najeriya, sbd kiyayya sun ma kasa lura da wannan.

Allah ya taimaki shugabanninmu ya kuma dawo da su lafiya.
Ameen.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button