Labarai

Sanatan Kano Ta Tsakiya: Kujerar Da Ba A Taba Maimaitawa Ba



*Ko Kwankwaso Zai Karya Wannan Tarihi?
Daga Maje El-Hajeej Hotoro, Kano
Siyasar Kano ta Tsakiya ita ce siyasar da ta sha daban da dukkan sauran yankunan Kano kasancewar babu wanda ya taba lashe zabe a karo na biyu. Duk wanda ya je sau daya ba ya kara koma wa. Hajiya Naja’atu Muhammad ta taba lashe kujerar, amma kuma guguwar juyin mulkin soji a shekarar 2003 ya haramta mata zuwa majalisa. Ta kuma kara fitowa da kokon bararta karkashin jam’iyyar ACN ana lika ta da kasa. Tsohon kakakin majalisar kasa Ghali Na Abba sau biyu ya na neman kujerar amma bai taba kai wa ga nasara ba. Ba mamaki yanayin kananan hukumomin da ta hada ne mai dauke da gogaggun ‘yan siyasa da kuma gawurtattun ‘yan Boko da attajirai shi ya sa kujerar ba a maimaita ta.
Sannan kuma kusan kananan hukumomin kwaryar birnin jihar Kano irinsu Municipal, Nassarawa, Dala, Gwale, Tarauni, Kumbotso, Fagge duk kusan nan ne cibiyar da ta tattara muhimman abubuwan ci gaban jihar da kuma rabin kudin shiga da jihar ke samu. Gwamna Malam Ibrahim Shekarau da ya mulki jihar tsawon shekaru takwas kana kuma ya yi takarar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar ANPP a shekarar 2011 na daga yankin Kano ta tsakiya. Kazalika Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso da ya mulki jihar a shekarar 1999 zuwa 2003. Kana kuma yanzu ya dawo a shekarar 2011 zuwa yanzu na daga wannan yankin. Muhammad Abacha da ya so tsayawa takarar jihar karkashin jam’iyyar CPC na wannan yankin. Kamar yadda Kanal Jafaru Isa tsohon gwamnan Kaduna a mulkin Soji da ya yi takarar gwamna a CPC dan wannan yanki ne. Bugu da kari Ibrahim Amin Little da ya yi takarar gwamna karkashin jam’iyyar PRP dan wannan yanki ne.

Riruwai da ya yi takarar gwamna karkashin jam’iyyar ACN dan wannan yanki ne. Kanal Habibu Shu’aibu tsohon gwamnan jihar Filato lokacin soji da ya yi takarar zaben cikin gida da Kwankwaso a shekarar 2011 a wannan yanki ya ke. Salisu Buhari Imam da ya zama kakakin majalisar wakilai dan wannan yanki ne. Ghali Na’abba shima daga wannan yanki ya maye gurbin sa. Ambasada Aminu Wali daya daga cikin iyayen da suka yi nakudar PDP a Nijeriya na wannan yanki. Kazalika tsohon dan gwagwarmayar siyasa Tanko Yakasai na wannan yanki. Dakta Akilu Sani Indabawa da ya ke bayar da shawara ga shugaban kasa dan wannan yankin ne. Ga kuma dattawan siyasa irin su Alhaji Lili Gabari da Ammani Inuwa. Dattijon Arewa kuma tsohon dan gwagwarmayar siyasa Tanko Yakasai anan ya ke. Bugu da kari nan ne cibiyar masarautar jihar Kano da kasuwanci. Kana kuma nan ne inda gidan Gwamna yake, kuma matattarar manyan attajirai.

Tsakanin Kwankwaso Da Lado
Sanata Basheer Lado Garba Muhammad ya zama zakaran gwajin dafin sauya siyasar yankin ba kamar Sanatocin da suka gabata ba. Attajirin dan kasuwa ne da aka haifa a 16 ga Octobar 1966. Wanda ya samu digiri a fannin kimiyyar siyasa a jami’ar Bayero da ke Kano. A shekarar 2007 da ya fito neman kujerar sanatan Kano ta tsakiya ya kaddamar da cibiyar Ladon Alheri Foundation da ya rika tallafawa talakawa da daukar dawainiyar gina makarantu, samar da rijiyoyin burtsatse da kuma yin tiyata ga masu matsalar ido kyauta. Kana kuma tare da daukar nauyin gasar karatun Alkur’ani mai tsarki. Duk da bai samu nasara ba, a shekarar 2011 ya kai ga samun wannan kujera da yawan kuri’u 359,050 karkashin jam’iyyar PDP.

Wani babban kudiri da ya cimma shine daukar dawainiyar gyara gadar Tamburawa da ya yi da kudin aljihunsa. Wannan gada dai ta kasance tsawon lokaci ta na ci wa matafiya tuwo a kwarya sakamakon rashin kyan ta. Kana kuma ta zama silar rasa rayukan mutane da dama saboda yawaitar hadari. Musamman ma kasancewar ta a muhimmin titin Kano zuwa Kaduna. Gyaran gadar da ta ke kusan kilomita 22 da biyu zuwa kwaryar birnin Dabo ya sanya natsuwa a zukatan matafiya tare da kyautata zirga zirga ababen hawa. Lado bai tsaya a nan ba, ya shiga ya kuma fita ya samar da gagarumin aikin gadar sama a daidai shatale talen asibitin kwararru na Malam Aminu Kano. Wannan ko shakka babu duk mai shiga jihar Kano ya san yadda ya ke hada kazamin cunkoso. Wanda yin gadar zai sa ta sauka fuska hudu daga Hotoro zuwa Court Road, kana kuma daga Na’ibawa zuwa gyadigyadi.
Wannan wani gawutaccen aiki ne da babu wani sanata da ya taba samo makamancinsa a duk sanatocin da aka taba yi a jihar Kano. Amma duk da haka a yayin da ya nemi sake maimaita wannan kujera ya fuskanci kaye mafi muni a tarihin siyasar wannan kujera. Kamar yadda yayi rashin sa’ar haduwa da mummunar adawar siyasar da ta taba mutuncinsa. Zuwa yanzu Lado na sansanar komawa jam’iyyar APC bisa zargin zai kara neman wannan kujera.
Kwankwaso

Ba ma a siyasar Kano ba, a Nijeriya ma yanzu Kwankwaso ba ya bukatar gabatarwa. Sai dai a duk lokacin da aka ambaci sunan Kwankwaso a jihar Kano, ba tare da bata lokaci ba zazzafar muhawara za ta kaure. Duk cikar siyasar Kano da batsewarta babu wanda sunan sa ya taba zama hantsi leka gidan Kanawa kamar Kwankwasiyya. Kusan kowane gida a jihar Kano sai ka samu akwai masu tsananta soyayya da Kwankwaso ko kuma zurfafa kiyayyar sa. Babu wanda idan ya yi magana ta ke zama abar yamadidi ta sigogi da dama kamar Kwankwaso. Babu dan siyasar da ya yi matsanancin bakin jinin da Kwankwaso ya yi a idon Kanawa kamar yadda babu gwamnan da ya ke da shakikan masoyan da suke tsasanin sonsa babu gudu babu ja da baya kamar ‘yan Kwankwasiyya. Wasu nakin jinin Kwankwaso ne saboda kallonsa da suke a matsayin mai takalmin karfen da zai iya taka uban kowa amma shi bai yarda kowa ya taka shi ba. Yayin da wasu ke matukar adawa da shi saboda kallonsa a matsayin kadangaren bakin tulun da ya hana su zama abinda suke son su zama a siyasa. Wasu kuma nakin Kwankwaso ne sakamakon karfen kafa da ya zamar musu ta hanyar hana su watanda da dukiyar talakawa. Yayin da wasu ke tsananta yin hassada da shi domin zamantowa da ya yi tamkar hasken ranar da hasken siyasarsa ya shafe na su. Wasu na hamayya da Kwankwaso ne domin rikar sa da suka yi a matsayin wanda idan ya samu dama zai murkushe tasirin alfarmar da suke da ita na juya gwamnati yadda su ka so.Lokacin da Kwankwaso ya zama gwamna cikin Kanawa da dama ya duri ruwa saboda tsananin tsanar da aka yi masa babu wanda ya zata Allah zai kara lamince masa. 

Musamman ma wadanda suka sha alwashin sai dai ya mulki makabarta amma ba jihar Kano ba. An biya duk irin kudaden da za a biya a kafafen yada labari domin karya kashin
bayan siyasarsa, amma hakan bai hana shi kaiwa gaci ba. Wani abin mamaki shine yadda gabadaya ya ba mutane mamaki ta hanyar cika kusan duk alkawuran da ya dauka a yayin yakin neman zabe.


Shine Gwamna na farko a tarihin siyasa da ya tafi da mataimakinsa lafiya lau ba tare da sun samu matsala ba. Kana kuma da ya kara dawowa ya kara dawo da shi bai sauya ba. Ganin ya na ba wa makiyansa kunya ya sa aka kunno wutar rikici tsakaninsa da Jonathan, wanda daidai da rana daya ba ya shakkar sa ballantana tsoron mayar masa da martani. Shine gwamna nafarko a jihar da aka kaiwa mahaifinsa hari domin firgita siyasarsa. Komawarsa jam’iyyar APC ya sa gabadaya siyasar Kano ta sauya sabon salo. Domin sai ga shi kusan fulogan Shekarau da a baya suka rika yakarsa sun zubar da makamansu sun koma bayansa. Kazalika kuma Shekarau ya tattara komatsansa ya tsallaka jam’iyyar PDP da a baya ya rika yakartawa ba dare ba rana sai ta kai a jihar Kano idan kana PDP kallonka ake yi a matsayin Musulmi mai matukar raunin imani.

Kwankwaso ya nemi kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya bayan ya Buhari yayi nasarar akan sa yayin gudanar da zaben fitar da gwani a takarar shugabancin kasa. Siyasar kujerar ta dau zafin da ba ta taba dauka ba, wanda a karshe yayi wa Lado mummunan kayen da ba a taba yi ba, kana kuma ya zama Sanata mafi yawan kuri’u a tarihin siyasar Najeriya. A yanzu da ya ke Sanata ya zama mafi farin jini a yankin Arewa bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari. A halin yanzu magoya bayansa na yi masa tayin shugaban kasa, yayin da gwamnatin jihar Kano da ya kafa yanzu suka koma abokan gaba na yunkurin hana shi maimaita wannan kujera. Shin zai maimaita ko tarihi ne zai maimaita kansa?

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button