Labarai

NAJERIYA Najeriya Tayi Hasarar Dalar Amurka Miliyan 100

Kimanin dalar Amurka Biliyan 100 ne Gwamnatin Najeriya, tayi hasara daga kudaden da take samu cikin shekaru biyu sakamakon karyewar farashin Man fetur a kasuwar duniya
Babban darakta mai kula da hukumar dake fitar da kayayyakin Najeriya domin sayarwa Mr. Olusegun Awolowo, ya ce faduwar farashin mai yasa Najeriya cikin halin matsin tattalin arziki. Ya furta haka ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai.

Yace karancin kudin da matsalar tattalin arziki da najeriya ke fuskanta ya samu ne dalili da hasarar dala Biliyan talatin zuwa arba’in, da Najeriya take yi a duk shekara a shekaru biyun da suka gabata lamarin da kuma ya haifar da matsalar tattalin arziki da ‘yan Najeriya, basu tsanmaci hakan ba.

A cewar Mr. Awolowo, idan har Najeriya, na bukatar fita daga wannan matsalar da take ciki to dole ne a bujuro da wasu hanyoyi na fitar da kayayyaki domin samun kudaden waje da kuma karfafa darajan Naira, sai kuma samun kudaden waje daga gwamnatin tarayya da kuma na jihohi wand aba na Man fetur ba.

Mr. Awolowo, yace yanzu haka hukumar dake kula da kayayyaki ta Najeriya, ta dukufa wajan ganin an samu kudaden shiga kimanin Triliyon daya da rabi zuwa Triliyon biyar a duk shekara lamarin da yace zai taimaka wajan farfado da tattalin arzikin Najeriya.

Masana tattalin arziki da wasu ‘yan Najeriya, kamar ita kanta Gwamnatin tarayyar Najeriya sunyi ittifakin cewa kumawa harkar gona shi ne mafita ga Gwamnatin Najeriya, inda hukumar dake kula da fitar da kayayyakin na Najeriya ta bayana cewa yanzu haka ta maida hankali wajen fitar da Koko da Yazawa da kuma Ridi abinda ke samun kasuwa matuka a kasashen yammacin Turai.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button