MTV:-Davido ya zama gwarzon mawakan Afirka
Mawakin Najeriya Davido ya lashe kyautar MTV da ake bayarwa a Turai a matsayin shahararren mawakin Afirka a gagarumin bikin da aka gudanar ranar Lahadi a London.
Davido ya doke takwaransa Wizkid da suke tashe a yanzu.
Sau biyu ke nan dai mawakan biyu ‘yan Najeriya ke takarar lashe kyautar.
Wakar Davido “IF and Fall”, ta samu karbuwa a shekarar 2017, inda a kwanan nan kuma ya saki sabuwar waka mai suna “FIA”.
Sai dai kuma Davido bai samu halartar bikin ba, saboda ya tafi wani aikinsa na waka a Luanda babban birnin Angola.
Amma mawakin ya bayyana farin-cikinsa a shafin Instagram inda ya godewa wadanda suka taimaka ya lashe kyautar da suka hada da mahaifiyarsa.
An gudanar da bikin bayar da kyautar ta MTV ne a Wembley, wanda shi ne karon farko da aka taba gudanar da bikin a London a tsawon shekaru 20.
Sauran mawakan Afirka da Davido ya doke sun hada da Nasty C, da Babes Wodumo, ‘yan Afirka ta Kudu da mawakin Kenya Nyashinski da kuma C4 Pedro na Angola.
Amman a taron bayar da kyaututtukan mawakan Afirka ta AFRIMA 2017 kuma ga wadanda suka samu kyaututtuka.
Gwarzuwar mawakiya a tsakiyar Afirka: Montess – da wakarta ta “Love Witta Gun Man.”
Gwarzon mawaki na tsakiyar Afirka: Locko – da wakarsa ta “Supporter” wadda suka yi tare da Mr Leo
Gwarzuwar mawakiya a gabashin Afirka: Nandy – da wakarta “One Day”
Gwarzon mawaki na gabashin Afirka: Eddy Kenzo – da wakarsa “Shauri Yako”
Gwarzon mawaki na kudancin Afirka: Emtee – da wakarsa “We Up”
Gwarzuwar mawakiya ta Afirka ta yamma: Tiwa Savage – da wakarta “All Over”
Gwarzon mawaki na Afirka ta yamma: Wizkid – da wakarsa “Come Closer” wadda suka yi ft Drake
Fitaccen mawaki na shekara: Davido – da wakarsa “Fall”
Wakar hadin gwiwa da ta fi fice: wakar Aje wadda Ali Kiba ya yi da MI
Wakar Afirka ta zamani da ta fi fice: wakar Isakaba da Wande Coal ya yi tare da DJ Tunez
Wakar hip hop ta fi fice ita ce :wakar Juice da Ycee ya yi.
Wakar Pop ta fi fice a Afirka: wakar Tere Tere wadda Toofan ya yi
Wakar Rock ta Afirka da ta fi fice: wakar Gilad – da Angel Uriel ya yi da Omer Millo
Mace da ti bayar da kwarin gwiwa: Asikey -a wakarta ta Earth Attack
Mai shirya waka da ya fi fice cikin shekara: DJ Coublon -wanda ya shirya wakar Yolo Yolo ta Seyi Shay
Wakar da ta fi fice a shekara: wakar Shauri Yako – wadda Eddy Kenzo ya yi
Wakar bidiyo da ta fi fice a shekara ita ce: Cooking Pot wadda Orezi ya yi, kuma Adasa Cookey ya bayar da umarni.