Labarai

Labari mai dadi:- Matasa Milyan 15 Za Su Samu Aikin Yi A Gwamnatin Tarayya

Advertisment


Daga Sheriff Sidi

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewar matasa milyan 15 za za su samu aikin yi a kokarin da take yi na bunkasa tattalin arziki.

Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Muhammadu Buhari kan Shirin Bunkasa Tattalin Arziki (Economic Recovery Development Plan) Malam Sani Yakubu ne ya bayyana hakan a wajen bude babban taron Majalisar Koli ta Harkokin Kasuwanci, Masana’antu da Saka Jari kashi na tara a yau Laraba a otel din Giginya da ke Sakkwato.

“Babbar manufa ita ce samun nasara a tattalin arziki ta hanyar raguwar hauhawar farashi, tsayayyen farashin musayar kudi da samar da hanyoyi ga ‘yan Nijeriya domin su shiga harkokin kasuwanci.” Ya bayyana.

Yakubu ya kuma bayyana cewar a karkashin shirin al’ummar Nijeriya za su ci gajiya a lamurran makamashi da sha’anin wuta da man fetur tare da bunkasa sufuri.

Ya ce ba abin mamaki ba ne yadda Kasuwanci, Masana’antu da Saka Jari ya zama daya daga cikin fannoni biyar da aka baiwa muhimmanci domin fita daga matsin tavarvarewar tattalin arziki a Nijeriya.

A jawabinsa Babban Sakataren Ma’aikatar Kasuwanci, Masana’antu da Saka Jari ta Kasa, Mista Edet Sunday Akpan ya bayyana cewar a baya-bayan nan Tattalin Arzikin Nijeriya ya fuskanci kalubale sosai musamman ta dalilin tabarbarewar Tattalin Arzikin Duniya bakidaya a bisa ga dogara kacokam kan man fetur.

Akpan ya bayyana cewar a yanzu haka Nijeriya ta fita daga kangin tabarbarewar tattalin arziki da kashi 0.55% wanda kuma yake karuwa.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button