Kannywood Sharhin Fim Din Rariya
Mafi yawan mutanen da suka rika zumudin a saki fim din “Rariya” a kasuwa ba komai ba ne yaja hankalin su ba illa wakar fim din wadda fitaccen mawaki Umar M Shariff ya rera. Hakika, fim din ya yi dacen waka tare da bidiyon wakar da aka dauka a cikin sa wadda Ali Nuhu da Rahama Sadau su ka yi wata irin salon rawa.
Na kalli fim din Rariya kuma ya kayatar sosai. Domin an yi amfani da kayayyaki na zamani, tun daga suttura har kayan da aka sanya a fim din sun dace.
San nan ya ankarar da iyaye masu barin ‘ya’yan su zuwa Makarantar gaba da sakandire. Sai dai labarin fim din an rika tafiyar hawainiya babu kuma kwallin kura a rubutun sa sannan kuma ana kwan gaba kwan baya ba tare da an ja zaren labarin yadda zai rikitar da masu kallo ba.
Domin kuwa duk wanda ya fara kallon fitowa ta daya zuwa ta biyu ko da bai ida kallon fim din ba zai fadi maka yadda fim din zai kare.
*An yi wakar idan ba muhallinta ba, domin ya kamata ace sai da Ali Nuhu ya shawo kan Zee lokacin aka yi wakar.
*Wasu kayan da Rahama ta sanya a wakar (Riga Blue) sam-sam basu dace ba, domin ana ganin surar jikinta.
*Bai kamata mahaifin Faty Washa bayan ya ga fuskarta ba a wurin faty, kuma a raina masa wayo, Ko a duhu uba ya laluba zai gane jininsa ya kamata a yi wata dabarar ba ta dauke wuta ba. *Wace Jami’a ce ake wata uku a semester daya? Kamar yadda Hafsat Barauniya ta fadi a fim din.
* A nuno Washa da Sadik na cikin mota suna tafiya amma ta ce wa babanta tana daki, shi wane irin mutum ne dai ba zai ji karar tafiya a mota ba.
* Wace jami’a ce a kasar nan ake hada da mata maza a hostel daya? Domin Lokacin da Rahama ta zo motar da aka bata a hostel din su an nuno wasu maza a kan bene bayan mun san cewa ko ziyara ba a yarda a shiga a hostel din mata ba.
*An samu matsalar wurin tantance ‘yan wasa (Auditioning) domin wanda aka nuno a matsayin Mahaifin Hafsat Barauniya ya yi karami.
*Shehu Hassan Kano da aka fiddo a matsayin kakan Zee ya kamata a yi masa kwalliyar da za ta nuna dattijankarsa, ba wai a nuno shi yadda ya saba fitowa ba.
*Har fim din ya kare ba a nuno makomar su Zaharaddini Sani ba da sauran tawagar sa. Ina makomar barayi a film din?
Mun dauko sharhin nan daga shafin @kannywoodexclusive