Kannywood

Kannywood : Ban Auri Hadiza Gabon Ba-Inji Ali Nuhu

Advertisment


Shahararren jarumin nan na Kannywood, Ali Nuhu ya karyata rade-radin dake yawo cewa ya auri jarumar Kannywood Hadiza Gabon cikin sirri.


Jarumin wanda aka fi sani da sarki mai Kannywood ya bayyana hakan ne a wani hira da yayi da jaridar Daily Trust.

Kwanan nan wani hoton Ali Nuhu da Gabon ya yi fice a shafukan zumunta inda ake ce jaruman biyu sunyi aure a Kano.


Ali Nuhu wanda ya kasance shugaban kamfanin FKD Film Production ya bayyana cewa wasu mutane na nan wanda burinsu shine yada jita-jita ba tare da tunanin abunda ka iya zuwa ya dawo ba.


Ya kara da cewa wannan hoto da ya haifar da jita-jita shirin wani fim ne mai suna ‘Akushi’ inda jarumar ta fito a matsayin matarsa.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button