Uncategorized

JI KA KARU: Me ka sani game da mutuwa? Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gummi


Hakika Fitan rai yana da wani irin radadi wanda babu mai saninsa sai dai Mamaci.. 

Mamaci yayin da ransa ya kusan fita, Muryarsa takan karye, Qarfin jikinsa yakan tafi.. Babu damar Eehu ko kururuwar zafin da yake ji. Domin zafin mutuwa ya riga ya ratsa dukkan sassan jikinsa.. 

Ba zai samu damar neman taimako ba, ballantana adauke masa zafin radadin da yake ji. Sai yayi fatan wannan nishin da yakeyi ko zai zama dalilun samun rangwame, amma inaa!!.

Idan har akwai ragowar wani Qarfi gareshi shine za’a rika jin wani irin gurnani yana fitowa daga chan cikin Qirjinsa da Makogoronsa yayin da rai yazo fita.. Alhali launin fuskarsa ya chanza saboda tsananin halin da yake ciki. 

Yayin da ranka yazo Makogoro, awannan lokacin zaka manta da Makusantanka, iyalanka ko ‘Ya’yanka, balle Makobta. Awannan lokacin ne ‘Dan Adam yakan ji wata irin Qishirwa mai tsanani wacce sai ya gwammaci inama ya bayar da dukkan abinda ya mallaka domin a bashi ruwan da zai kurba koda kurbi guda ne!!.

A wannan lokacin duniya da dukkan abin cikinta zasu zamanto ba komai ba… Ballantana dukiya ko Mulki ko wani gata… ‘Dan Adam zai gane cewa ashe shi ba komai bane.. Kuma tun daga sannan zai fara nadamar lokutan rayuwarsa da suka tafi wajen sa’bon Allah!! 

Tunda Shugaban Halitta (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya ‘dan’dana zafin mutuwa, Ka sani cewa kaima sai ka ‘dan’dana!! 

Imamul Bukhariy ya ruwaito daga Nana A’isha (rta) tana bayar da labarin jinyar da Manzon Allah (saww) yayi adakinta, har zuwa rasuwarsa. Tace :

“Hakika Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya kasance a gabansa akwai wata guga wacce akwai ruwa acikinta, yana shigar da hannayensa acikin ruwan sannan ya shafe fuskarsa dasu. Yana cewa :

“LA ILAHA ILLAL LAAH!! HAKIKA MUTUWA TANA DA RADADI!”.

Sannan ya chira hannunsa sama yana cewa : “ACIKIN TAWAGA MADAUKAKIYA!”. (Alokacin an bashi za’bi ne tsakanin ci gaba da zaman duniya, ko kuma komawa zuwa ga Ubangijinsa). 

Yana fa’dar haka har sai da aka karbi ransa sannan hannunsa ya karkato…

Annabi Muhammadu kenan (saww) Shugaban halittun Allah baki daya, wanda bai ta’ba sa’ba ma Allah ba. ballantana kai wanda kullum acikin sa’bon kake kwana kake tashi. 

Lokacin da Amru bn Al-As (ra) yazo rasuwa, an tambayeshi shin yaya yake ji?.  Sai yace “Ji nakeyi tamkar sammai sun fa’do akaina, Qassai kuma sun matseni”.

Sayyiduna Umar bn Al-Khattab (ra) ya tambayi Ka’abul Ahbari ya siffanta masa yadda mutuwa take. Sai yace : “Ya Kai Sarkin Muminai! Hakika ita mutuwa kamar wani reshe mai yawan Qayoyi ajikinsa, ashigar dashi cikin cikin mutum. Bayan kowacce Qaya ta rike wata jijiya daga jijiyoyin jikinsa, sai kuma a samo wani mutum Ma’abocin Qarfi, ya kama wannan reshen ya fizgoshi da Qarfi, ya fizgoshi kenan tare da tsoka da jijiyoyin jikin!!!.

Yanzu ‘Yan uwa koda tunanin wannan ranar bai ishemu dalilin rage sa’bon Allah ba!!. 

Wannan ranar fa sai ta riskeni, sai ta riskeka, sai ta riskeki, sai ta riskemu baki dayanmu kamar dai yadda ta riski wadanda suka rayu kafinmu.

Daga cikin abubuwan dake haddasa tsananin zafin fitan rai tare da gigicewa akwai :

– Wulakantar da Sallah. 
– Wulakanta Mahaifa. 
– Chutar da Manzon Allah (saww) ko iyalan gidansa da zuriyarsa ko kuma Sahabbansa (Radhiyallahu anhum).
– Cin Mutuncin Malamai Waliyyai da salihan bayin Allah. 
– Shan giya ko Miyagun Kwayoyi. 
– Cin haram (Cin hanci, wawure kudin gwamnati ko Kudin Marayu, ko Satar dukiyar jama’a, etc). 
– Kisan rai ba tare da hakki ba. 
– Zina, Luwadi, Madigo. 

Ya Allah ka kiyayemu daga Mummunar mutuwa. Ameen.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button