Falana Ya Sake Rokon Buhari Kan Ya Saukakawa El Zakzaky Kuncin Da Yake Ciki
Fitaccen lauyan nan, Femi Falana ya sake rubutawa Shugaba Muhammad Buhari wasika inda ya roke shi kan ya bayar da umarni a saki Shugaban Kungiyar Shi’a, Malam Ibrahim El Zakzaky saboda ya je kasar waje don a duba lafiyarsa shi da uwargidansa Malama Zainab wadda har yanzu akwai harsashi a jikinta.
A cikin wasikar, Lauyan ya ja hankalin Shugaba Buhari kan cewa El Zakzaky ya rasa idonsa guda kuma a halin yanzu dayan idon na fuskantar barazana kuma iyalansa sun nemi a ba su izini su shigo da kwararren likita daga waje don a duba idon amma kuma jami’an tsaro na DSS sun ki amincewa.
Lauyan ya kara da cewa kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin malamin tare da biyansa diyyar Naira Bilyan 50 amma kuma gwamnatin tarayya ta ki mutunta wannan hukuncin kotun inda ya nuna cewa hakan zai sa a dauki gwamnatin a matsayin wadda ba ta mutunta tsarin doka.
Rahoto:- Daga Rariya