Labarai

Addu’a Ya Kamata Jama’ar Jihar Kaduna Su Yi Akan El Rufa’i Na Allah Ba Shi Lafiya, Inji Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa

Daga Ibrahim Ammani Kaduna 

An yi kira ga illahirin Jama’ar Jihar Kaduna kwata da cewar, su mike gaba dayansu Musulmai da Kiristocin su sanya Gwamnan Jihar El Rufa’I cikin addu’o’insu domin ganin ya samu lafiya daga halin da yake ciki, domin yanayin da Gwamnan ya ke ciki a yanzu, yanayi ne irin na mai fama da matsalar kwakwalwa, kuma yake bukatar taimakon gaggawa ta addu’ar jama’a. 

Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa 16 wadanda suka taba bada wa’adin korar Inyamurai a watannin baya da suka gabata ne suka yi wannan kiran, a yayin wani taron manema labarai da suka kira a garin Kaduna. 

Mai magana da yawun Matasan Alhaji Ashiru Sheriff yace kiran na su ya zama wajibi ne idan akayi la’akari da salon kamun Ludayin Gwamnan,  inda ya zamana ya daura damarar Yaki da kowa a jihar, bai bar Ma’aikatan Gwamnati ba,  bai bar Sarakuna ba, bai bar ‘Yan siyasa ba, bai bar ‘Yan kasuwa ba, bai kyale talakawa ba, to wannan babbar alama ce da ke nuna cewar da akwai matsala ta kwakwalwa ga Gwamnan, kuma Masoyan Gwamnan na gaskiya sune za su bukaci a aiwatar da Addu’a ga Gwamnan. 

Shugaban Matasan ya bada misali da wani Shugaban da aka taba yi a kasar Nijar wanda ya samu matsala ta kwakwalwa na tsawon shekaru uku amma ba’a gane ba, yayi ta musgunawa jama’a yana karan tsaye ga dokokin kasa, sai a ranar da asiri ya tonu wannan Shugaba ya shigo Ofishin shi ba ta inda ya kamata ya shigo ba, sannan ya durkusa kasa ya gaishe da Sakataren shi,  wannan abu shi ne ya bayar da tsoro ga mukarraban Gwamnatin shi, aka dauki matakin fita da shi waje, bayan an yi gwaji aka gano cewar yana fama da matsalar tabin hankali na tsawon shekaru uku, a bisa ga wannan dalili ya kamata jama’a su yi tunani akan abinda ke faruwa a jihar Kaduna, sallamar Ma’aikata har sama da Dubu Ashirin a lokaci guda abu ne da hankali ba zai dauka ba Inji shi. 

Dangane da kiran su da sunan ‘Yan ta’adda da El Rufa’I yayi a yayin zantawar shi da manema labarai a kwanakin baya kuwa, Matasan sun bayyana cewar sanin Dan ta’adda a tsakanin su da Gwamnan a fili yake, domin duniya ta shaida cewar su ne suka bada Wa’adin korar Inyamurai daga Arewa, amma bayan kiran su da akayi da basu baki, sai suka janye matakin da suka dauka kuma babu wani Inyamurin da aka taba a yankin Arewa, amma jama’a sun shaida irin kira da roko da akayi tayi wa Gwamnan na kar ya rushe gidajen jama’a, kada ya kori Ma’aikata a jihar, amma duk yayi kunnen uwar Shegu akai, saboda haka wanene Dan ta’adda a tsakanin su, Matasan Arewa ne ko kuma Gwamnan??

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button