Jarumar kannywood Aisha Tsamiya Za Ta Yi Karatu a Jami’ar NOUN
Ba mu yin Health Technology, inji jami’ar
Fitacciyar jaruma A’isha Aliyu (Tsamiya) ta bayyana cewa ta samu gurbin karo karatu a Budaddiyar Jami’ar Njeriya, wato National Open University of Nigeria (NOUN).
A wata hira da aka yi da ita a gidan talbijin na Arewa24, jarumar ta bayyana cewar za ta karanta kwas din ‘Health Technology’ ne.
A amsar wata tambaya da mai gabatar da shirin “Kundin Kanbywood”, wato Aminu A. Shariff (Momoh), ya yi mata, A’isha ta ce, “Yanzu na samu admission a Open University… Ina so in karanci Health Technology.”
To amma mujallar Fim ta gano cewa ba a yin wannan kwas din a jami’ar.
Daraktan Watsa Labarai na jami’ar, Malam Ibrahim Sheme, ya fada wa mujallar Fim cewa, “Health Technology bai cikin jerin kwasakwasan da wannan jami’ar ke gudanarwa. Amma kwas din da jami’ar ke yi wanda ya kusanci abin da A’isha Tsamiya ke so ta karanta shi ne ‘Public Health’.”
Daraktan ya ce ya ji dadin kudirin A’isha na zurfafa karatun ta, musamman a NOUN. Ya ce yin hakan ya nuna cewa ita mace ce mai hazaka tare da kokarin inganta rayuwar ta.
Ya ba ta shawarar cewa ya kamata ta zabi kwas din da jami’ar ke gudanarwa, kuma an lissafa su a gidan yanar jami’ar, wato www.nouedu.net.
Sheme ya yi kira ga sauran ‘yan fim da su yi kokari su je jami’ar Open University domin su zurfafa karatun su. Ya ce karatu a NOUN ba sai sun bar ayyukan da ke gaban su ba, domin shi karatun daga ko’ina mutum ya ke zai iya yin sa.
“Ba sai mutum ya tafi aji ba yadda ake yi a sauran jami’o’i,” inji shi. “Haka kuma akwai rage kashe kudi fiye da na sauran manyan makarantu.”
Ita dai NOUN, ta na daga cikin manyan jami’o’in Gwamnatin Tarayya. Daliban ta sun fi na kowace jami’a yawa a duk fadin Afrika ta Yamma, ba ma Nijeriya kadai ba.