Labarai

Har Yanzu Buhari Na Da Sauran Dama Ta Gyara Nijeriya Bisa Alkawuran Kamfen Din 2015, Inji Attahiru Bafarawa

Daga Ibrahim Baba Suleiman
Tsohon gwamnan Sokoto Attahiru Dalhatu Bafarawa ya ce shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na da sauran dama ta gyara Najeriya bisa alkawuran kamfen din 2015 da ya dauka na inganta tsaro da tattalin arziki.
Bafarawa wanda yake zantawa da manema labarun ketare a Abuja, bai gamsu da bugun kirjin gwamnatin APC mai da’awar canji ba cewa ta samar da ingantaccen tsaro, ya na mai buga misali da kalubalen satar mutane da ma labarun yadda ‘yan Boko Haram kan kai hare-hare.
“A gani na shugaban ya na da sauran lokaci da zai gyara kasar kamar yadda ya yi alkawari, kuma mun yi farin ciki da yadda ya samu sauki daga jinyar da ta kai shi London”
Kodayake tsohon gwamnan na jam’iyyar adawa ta PDP, ya ce adawa mai amfani itace mutum ya ga inda a ka samu kuskure ya ba da shawari tsakani da Allah yadda za a samu gyara saboda amfanin dinbin talakawan Najeriya ba tare da nuna wariyar kabila ko yanki ba.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.comMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button