Dan Sanata Yayi Barazanar Harbe Ladan Da Liman Saboda Damunsa Da Kiran Sallah
Dan gidan Sanata Bala Ibini Na’Allah yayi yinkurin Harbe Limamin Unguwar su da Aladani da Bindiga wai suna damun shi da kiraye-kirayen Sallah idan yana hutawa.
Murtala Bala ibini Na’Allah wanda shine Dan gidan Sanata ya fito da Bindiga rike da karnuka a hannun sa yazo har kofar masallacin yana nuna Limamin da Ladanin sa da Bindigar yana gargadar su yana cewa kodai su dena damun shi da kiran Sallah ko kuma ya dauki mataki.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewar hakan ta Faru a Jihar Kaduna a kan Titin Zobe Road dake cikin Unguwar Rimi ta Jihar Kaduna a ranar Laraba 4-10-2017 da yamma gabanin Sallah Magariba.
Wani wanda hakan ta faru a gaban shi ya bayyanawa wakilin mu Shuaibu Abdullahi cewar bai taba ganin Izgilanci irin wannan ba.
Haka kuma yace masallacin shi kadai ne a kan Titin Zobe Road a Unguwar Rimi kuma sunan Limamin Malan Isah.