Buhari Ya Nada Gwamnan JIGAWA A Matsayin Shugaban Kwamitin Da Zai Samo Hanyar Da Za A Tara Dala Bilyan 30 (30 billions)
Daga Engr Magaji Abdullahi Mallammadori
Domin inganta Kuɗin Shiga daga ɓangarorin da ba na albarkatun mai ba, Shugaba Buhari ya naɗa Gwamna Badaru ya jagoranci Kwamiti da zai samo hanyar da za a tara Dala bilyan Talatin daga ɓangarorin da ba na mai ba.
Domin sake fasalin tattalin arzikin Najeriya, gwamnatin tarayya ta ƙudurci aniyar samar da aƙalla Dala Biliyan 30 daga ɓangarorin da ba na albarkatun mai ba, wanda hakan zai samar da ƙarin Dala Biliyan 25 daga Dala Biliyan 5 da ake samu a halin yanzu.
Darekta Janar na Hukumar Bunƙasa Kayayyakin da ake fitar da su Ƙasashen Waje Segun Awolowo ne ya sanar da haka bayan kammala taron Majalisar Tattalin Arziki na Ƙasa wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta a fadar Shugaban Ƙasa.
Domin cimma wannan burin, fadar ta Shugaban Ƙasa ta kafa wani Kwamiti da zai zaƙulo hanyoyin da za a samar da waɗannan kuɗaɗen shiga daga ɓangarorin da ba na albarkatun mai ba, bayan tattaunawa da muhawarori da aka yi yayin taron Majalisar Tattalin Arziki na Ƙasa.
Awolowo yace an kafa wannan Kwamiti ne a shirin da gwamnati ke yi na daina dogaro da kuɗaɗen shiga da take samu daga albarkatun man fetur da samar wa Najeriya ƙarin kuɗin asusun ƙasa da ƙasa na Dala Biliyan 150 nan da shekaru goma, samar da ayyukan yi ga mutum 500,000, fitar da ƴan Najeriya sama da Miliyan 10 daga ƙangin talauci da kuma baiwa duk wata Jiha damar fitar da kayayyakin da take sarrafawa zuwa Ƙasashen ƙetare.
Abinda wannan shiri ya sanya gaba shine fitar da kayayyakin masarufi da albarkatun gona da suka haɗa da shinkafa, alkama, masara, Kwakwa, roba, fatu da ƙiraga, sukari, waken soya da kayayyakin motoci da sauran su zuwa Ƙasashen da Najeriya take hulɗar kasuwanci da su irin Holland, Sin, Iran, Jamus, Ingila, Faransa, Andalus, Italiya, India, Saudi Arabia da sauran su.
Sauran Mambobin Kwamitin sun haɗa da gwamnonin Lagos da Ebonyi wato Akinwunmi Ambode, da Dave Umuahia, Ministocin Masana’antu, Cinikayya da Zuba Jari, Albarkatun Noma da Raya Karkara, Wuta, Ayyuka da Gidaje, Sufuri da Kuɗi.
Sauran sun haɗa da hukumomin NEPC, NEPZA, Bankin NEXIM, Babban Bankin Najeriya (CBN).
Ana sa ran Kwamitin zata miƙa rahoton ta na farko a watan Nuwamba mai zuwa.