Taƙaitacen Tarihin Jarumar kannywood Halima Atete
Halima Atete ta dade da fara harkara fina-finan Hausa, amma ba tayi suna sosai ba Yar asalin Jihar Borno ce. Tauraruwar kan fito a matsayin wata muguwa a wasa kusan a ko yaushe.
Halima Yusuf Atete ba fim kadai ba tayi karatun law har zuwa matakin Diploma, ta fara karatun ta ne da fari a Garin Maiganari daga nan kuma ta koma wata Makarantar Gwamnati da ke Yerwa.
Daga baya ma ta koma Kwalejin nan ta Mohammed Goni inda tayi difiloma a shari’a.
Kamar yadda ta bada labari, tace tana ganin su Ali Nuhu da wani Directer wanda abokin yayanta ne Ahmed A Bifa sunzo Gidansu daukar fim, sai taji tana sha’awar shiga harkar,
To bayan ta samu kudinta shine ta taho KANO wajen wata babarta, zuwa wani lokaci sai dai aka ganta a fim wanda babanta yaso ya hana amma daga baya ya hakura ya kyaleta.
Halima ta fito a fina-finai irin su Kona Gari, Asalina, Dakin Amarya, Hannu da Hannu, Maza Da Mata dss. tayi fina-finai sun kai 150.
Ta kai an taba bata kyauta na ‘Yar wasar da ta fi kowa a cikin shekarun nan.
Atete tana taimakawa wadanda rikicin Boko Haram ya shafa a Garin su.
Yanzu haka kuma ta kafa wata Gidauniya Domin taimakawa kananan yara.
Halima yar Real Madrid ce ta mutuwa yanzu haka kuma tana Makkah domin yin aikin Hajji.