Kannywood

Masoyan Ali Nuhu Sun Kutuntumawa Rahama Sadau Ashariya

Binciken da muka yi ya nuna mana cewa su dai magoya bayan Ali Nuhu Mohammed suna hakan ne domin zargin jarumar da yi wa ogan na su zagon kasa. Wanda a ganin su ita jarumar tana yin zagon kasan ne don an ki a sanyata a cikin jerin jaruman da za su fito a fim din FKD na gaba mai suna ABOTA, sai aka sanya wadda basu shiri da ita wato Nafisa Abdullahi.

Wata majiya ta tabbatar mana da cewa tuni dai duk wani makusancin Ali Nuhu da mukarrabansa a ka sanyasu  su ka yi ‘Unfollowing’ din Rahama Sadau a shafin su Instagram.

 Yanzu haka dai magoyan bayan Ali Nuhu sun sanya  damarar Rigima da Jarumar a shafukan su na yanar gizo.

Ga kadan daga cikin rubututtukan wasu:

“Wallahi duk wanda ya taba Ali Nuhu sai Inda karfina ya kare, an yi walkiya mun ganki “

“Kin manta lokacin da kike cikin wahala aka fito da ke a cikin mutane”

” Kin manta lokacin da aka fifitaki akan kowa? Kin manta lokacin da wulakantaki shi din da kike Zagi ya rufa maki asiri?

“To, Wallahi ki shiga taitayinki, ki kuka da kanki. Don wallahi muna jiranki sai kin maimaita duk abin da kika fadi.

” Kuma kin yi kan ki kar ki kara cewa shi babanki ne shi wawuya…

KORARRIYA.

Sauran labaran za su biyo baya.

Sources Daga Shafin Kannywood Exclusive

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button