Labarai
Gwamnati Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’o’i
Gwamnatin tarayya ta cimma yarjejeniya da kungiyar malaman jami’o’i wadanda ‘ya’yanta ke yajin aiki kan kin biyansu wasu bukutunsu da gwamnati ta yi masu alkawari a can baya.
Sai dai Shugaban kungiyar na Kasa, Abiodun Ogunyemi ya nuna cewa Uwar kungiyar za ta tuntubi rassanta na jami’o’i wanda a wannan mataki ne za su yanke shawara game da janye yajin aikin.