Labarai

Tsohon Gwamnan Sokoto Ya Nesanta Kansa Da Kwankwasiyya

(Daga sani Twoeffect Yawuri.)
________£________

Wata drama ta barke yayin da tsohon gwamnar sokoto kuma dan majalisa mai wakiltar sokoto ta Tsakiya, Aliyu Magatagarda  wamakko ya fito fili karara ya neasanta kansa da akidar kwankwasiya da jar hula da ma kowace irin alama inda yace shi alamarsa ita ce APC.

Sanata wanda yake cikin fushi yace ni ba ni da  wata alama, alamata ita ce APC ba jar hula ba ko jar babbar riga. Ya kuma gargadesu da su daina alakantashi da jar hula inda ya ce yin haka kamar cin mutunci ne. Faruwar hakan ya sanya dar-dar a zuciyoyin mabiya darikar ta kwankwasiya a Sokoto wacce dan majalisar jihar, Galadanci Muhammad Bajare yake jagoranta.

Sources:Facebook/Rariya

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button