Labarai

AMINCI Da ALHERIN ALLAH Su Kai Ga Marigayi Umaru Musa Yar’adua

Daga Maje El-Hajeej Hotoro

1. Shugaban kasa na farko da ya rage kudin man fetur a Najeriya 

2. Shugaban kasa na farko mai Digiri a siyasar Najeriya 

3. Shugaban kasa na farko da ya kafa gwamnatin hadaka a siyasar Najeriya 

4. Shugaban kasa na farko da ya fara bayyana kadarorin sa a gwamnatin siyasa 

5. Shugaban kasa na farko da ya assasa Ajandoji 7 da ya ke Najeriya ta cimma a 2020

6. Shugaban kasa na farko da ya bayar da umarnin yashe Teku zuwa Arewa 

7. Shugaban kasa na farko da yayi ikirarin an tafka kuskure a zabensa 

8. Shugaban kasa na farko daga kujerar
Gwamna ya zarce ta shugaban kasa a Najeriya 

9. Shugaban kasa na farko da a lokacin da ya bar kujerar Gwamna ba wanda ya kai shi tara kudi a asusun gwamnatin jiharsa 

10. Shugaban kasa na farko da a lokacin da ya ke Gwamna duk Arewacin Najeriya ba Gwamnan da ya kai shi aiki. 

11. Shugaban kasa na farko da ya zauna da malaman jami’o akan su bullo da tsarin da za a gyara ilimi a daina kai ‘yan Najeriya kasar waje karatu.

12. Shugaban kasa na farko da ya kaddamar da yakin share kungiyar Boko Haram bayan tsawon shekaru suna cin karen su ba babbaka a Najeriya. 

13. Shugaban kasa na farko a Najeriya da ya sulhunta rikicin Neja Delta suka daina lalata kadarorin kasa. 

14. Shugaban kasa na farko da har yau ba wata hukumar yaki da cin hanci da rashawa da ta zarge shi ko Iyalansa da satar dukiyar talakawa. 

15. Shugaban kasa na farko a Najeriya da Mulki ne ya neme shi ba shi ya nemi mulki ba. 

16. Shugaban kasa na farko da ya furta cewa, shi Mutum ne kamar kowa kuma rayuwa da mutuwarsa na hannun Allah Madaukakin Sarki. Idan Ya so Ya raya shi idan Ya so Ya karbi ransa. 

Allah Ya Jikan sa Ya kuma gafarta masa.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button