Labarai

Allah Wadarai Da Kasashen Da Suka Yi Shiru Da Halin Ko In Kula Kan Musulman Burma, Cewar Rashida Mai Sa’a


Fitacciyar Jarumar Fina-Finan Hausa Rashida  Adamu (Rashida Mai Sa’a) ta yi “Allah wadarai da halin ko in kula da wasu Gwamnatocin kasashen Musulmai sukeyi dangane da Abubuwan da suke faruwa a Burma/Rohingya, Yakamata su dauki matakin dazai kawo karshen zuwan wannan Al’amarin a nan gaba”

“Idan za ku iya tuna abinda ya faru, a cikin watan Yuni na shekarar da ta gabata ne wani musulmi dan kasar Amurka mai suna Omar Mateen ya kai wani farmaki a wani gidan rawa inda yan luwadi suke taruwa suna rawa tare da badala a garin Orlando na Cikin kasar America, Cikin Ikon Allah ya kashe sama da mutane 50 daga cikin su”.

“Idan har mai karatu zai iya tunawa a lokachin ne  shugabanin kasashen duniya cikin gaggawa ba tare da yin wani jinkiri ba suka aika sakon jaje zuwa ga kasar Amurka har ma suke bayyana hakan a matsayin mummunan aikin ta’addanchi tare da yin tir da kuma Allah wadai ga haka.

“Tun a cikin shekaru fiye da 200 da suka wuce, akwai Musulmai a yankin Arakaan wanda adadinsu ya haura kimanin milyan 3 ko 4 a yayin da mabiya addinin Buddah adadin su ya kai su milyan 50, an kone musu gidajen musulmai masu dimbin yawa, an kuma yi wa malaman su kisan wulakanci. Da yawa daga cikin su sun bar gidajen su, wasu a hanyar ceton rayukan wasu,  sun rasa nasu rayukan, amma sai a yanzu ne abubuwan suke kara fitowa fili.

“Shin amma me ya sa har yanzu shugabannin kasashen duniya ba su furta komai dangane da irin kisan kiyashin da ake yi wa Musulman Burma/Rohingya ba?

“Amma kuma sun yi saurin aikawa da sakon jaje dangane da abinda Omar Matee ya aikata.

“Shin su ba Musulmai bane? Ko su an mayar dasu saniyar ware ne?

“Duk Musulmin dan Uwan Musulmi ne.

Ya kamata a ce irin wadannan tambayoyi suna yin shawagi a cikin kwakwalwar mu”


Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.comMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button