Kannywood

Nafisa Abdullahi tayi kaca-kaca da Rahma Sadau


Labarun da muke samu daga majiyoyin mu da dama na nuni da cewa da alamu takun sakar da ke a tsakanin manyan jarumai mata a masana’antar Kannywood watau Rahma Sadau da Nafisa Abdullahi na shirin daukar sabon salo.

Majiyar tamu dai ta ruwaito cewa a cikin wata fira da tayi, Nafisa Abdullahi ta bayyana cewa ita a wurin ta Rahma Sadau ba kowa bace don haka kuwa ba ta isa tayi gasa da ita ba.
Haka Kuma Arewarmu.com Ta samo daga NAIJ.com dai a wani bincike da tayi ta gano cewa rashin jituwar dake a tsakanin jaruman biyu ya samo asali ne a wattanin baya tun lokacin da za’a fara shirin fim din Rariya na Rahma Sadau din da aka ce ta gayyaci Nafisa Abdullahi amma taki yadda tayi bayan kuma ta karbar mata makudan kudade.

Binciken namu kuma ya bayyana cewa hakan ne ma ya sanya jarumar Rahma Sadau ta maka Nafisa Kotu domin a bi mata hakkin ta inda daga nan kowa ya ja daga cikin su yana zafafan kalamai ga yar uwar ta.

Source: Naij.com Hausa

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.comMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button