Kannywood

Yadda na ji rauni a fim din Dakin Amarya —Aisha Tsamiya

Aisha TsamiyaHakkin mallakar hotoAISHA TSAMIYA
Image captionAisha ta ce tana daukar fim a matsayin sana’a

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood, Aisha Aliyu, wacce aka fi sani da suna Aisha Tsamiya ta shaida wa BBC cewa babu fim din da ya taba ba ta wahala kamar “Dakin Amarya”.
Fim din Dakin Amarya yana magana ne kan yadda mata ke bakin kishi, musamman idan aka auro musu abokiyar zama – ta fito ne a matsayin kishiyar Halima Atete, wacce ita ce uwar gidan Ali Nuhu.
“Sai da na ji rauni na gaske a fim din musamman saboda yadda aka rika yin fatali da kayan daki irinsu tangaran da talabijin. Kai har kwanciya na yi a asibiti”, in ji Aisha Tsamiya, a hirar da ta yi da Nasidi Adamu Yahaya.
A cewarta, “Na dauki yin fim a matsayin sana’a don haka ina jin dadin fitowa a cikinsa.”
Aisha Tsamiya da Ali NuhuHakkin mallakar hotoYOUTUBE
Image captionAisha Tsamiya ta ce tana jin dadin yin fim da kowane dan wasa

Tsamiya, wacce ta soma fim a shekarar 2011, ta kara da cewa dukkan jaruman da ke yin fim tare da ita suna burge ta “kuma ina zaune da kowannensu lafiya”.
“Jarumai irinsu su Adamu (Adam A. Zango), Sadiq Sani Sadiq, Zahraddeen Sani, da dukkansu sauran jarumai suna burge ni. Haka ma mata jarumai, dukkansu ina zaune da su lafiya kuma suna burge ni”, in ji Aisha Aliyu.
Ta ce ta soma fitowa a fim din Tsamiya ne shi ya sa aka sanya mata wannan suna.
Aisha dai ta fi fitowa a fina-finan da ke nuna ta a mutuniyar kirki, wacce kuma ake tauyewa hakki.
Halima Atete

Hakkin mallakar hotoYOUTUBE
Image captionHalima Atete ce uwar gida a fim din “Dakin Amarya”
© bbhausa.com
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.comMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button