Addini

Ƙasar Saudiya Za Ta Kafa Cibiya ta Yaƙi Da Wahabiyanci Da Salafiya – Rex Tillerson


Ƙasar Amerka ta shawo  kan Saudiya kan ta janye goyon bayan da take bai wa aƙidun Wahabiyanci da Salafiya. Wannan yarjejjeniya ce wacce ƙasashen  biyu suka cimma a ziyarar da Shugaban Amerka, Donald Trump ya kai  Saudiya.

Amerka ta ce Saudiya ta riga ta kafa cibiya wacce za ta riƙa gudanar da shirye-shirye waɗanda za su share tsoffin aƙidun da maye su da sabuwar aƙida wacce ba za ta haɗa da abubuwan da suke sa yaɗuwar ta’addanci  a duniya ba.

Ta yaya wannan sabon shiri na Saudiya zai shafi addini da siyasar Musulmi a duniya?

Ina ga ya kamata al’ummar Musulmi su san abin da ke tafe.

A nan ƙasa, na fassara bayanin Rex Tillerson, Sakataren Harkokin Waje na Amerka, da ya yi kan wannan batun lokacin da yake kare abin da ya shafi bangaren harkokin ƙasashen waje na kasafin kudin 2018 na Shugaba Trump a majalisar Amerka. Na fassara shi  ne daga wani video na zaman majalisan wanda wani ɗan’jarida daga ƙasashen  waje ya aiko min.
_______

Tambaya:

A ƙarshe, a tambayar da ta wuce, Chairman, batun yarjejjeniya da ƙasar Saudi Arabia, ban sami amsa kan takammar hanya da (Amerka) za ta bi ba wajen tabbatar da cewa ƙasar Saudia ta daina goyon bayan yaɗa Wahabiyanci da Salafiya da kuma ta’addanci da ra’ayin waɗannan fahimta ta Musulunci ke jawowa a duniya. Ka san da wasu hanyoyi da ma’aikatarka take bi don auna ikrarin cewa tana bibiyar wannan? Ta yaya muke auna haka? Ta yaya za mu san cewa suna cika wannan sashinsu na alƙawarin?

Amsa:

Ɗaya daga cikin abubuwan da aka cimmawa a taron Riyadh da Shugaba (Trump) ya halarta shi ne samar da wata cibiya wacce za ta yi yaƙi da yaɗa matsanancin ra’ayin addini. Akwai wannan cibiya yanzu. An ƙaddamar da ita lokacin da muke can. Cibiyar na da shirye-shirye da dama waɗanda za su yi yaƙi da tsananin ra’ayin addini a duniya.

Ɗaya daga cikin waɗannan shirye shirye da muka yarda da su a kai shi ne – kuma sun riga sun ɗau mataki (su ƴan Saudiya) – buga sabbin litattafai da za a yaɗa a makarantu da masallatai a duniya. Litattafan za su maye litattafan da ke nan yanzu waɗanda suke yaɗa zazzafar fahimtar Wahabiyanci da halatta tashin hankali. Mun ce musu kar kawai su buga sabbin litattafan, amma su dawo da tsoffin ma. Wannan misali ne kawai guda ɗaya.

Cibiyar za ta gudanar da ayyuka masu yawa da suka shafi kafofin sada zumunta, da kafofin watsa labarai, zuwa kuma yadda ake horar da ɗalibai limamai a makarantun addini.

______
Dr. Aliyu U. Tilde
5 Agusta 2017

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button