An Kama Bayahuden Da Ya Yi Badda Bami Yana Limanci
Jami’an kasar Libya sun sanar da cewa mutumin da suka kama a matsayin kwamandan kungiyar Da’esh, yana aiki ne da kungiyar leken asirin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ne ta Mosad.
Tashar telbijin din al-jadid ta kasar Lebanon ta bada labarin cewa; limamin masallacin mai suna “Abu Hafs” an kama shi ne a garin Banighazi da ke gabacin kasar Libya. Binciken da aka gudanar akan shi ya tabbatar da cewa mutumin bayahude ne dan haramtacciyar kasar Isra’ila kuma sunanshi na gaskiya shi ne; Benyamin Afrahim.
Jami’an gwamnatin kasar ta Libya sun tabbatar da cewa; Afraham yana a karkashin rundunar leken asiri da ake kira “Masu kama da larabawa’ da ke karkashin Mosad, aikinsu kuwa shi ne yin leken asiri a cikin kasashen larabawa.
Afraham ya shiga kungiyar Da’esh, har ta kai shi ga zama kwamanda da mayaka 200 a karkashinsa, kafin daga baya ya zama limamin masallaci a Banighazi.
Rahotanni sun nuna cewa aga cikin manufofinsa shi ne bude yaki a cikin kasar Masar.