Kannywood

Nayi nadamar fitowa a akasarin fina-finan da na yi — Jarumi Adam A Zango

An hana ni aure saboda zargin luwadi – Adam A. Zango

  • Akwai sautin cikakkiyar hirar da BBC ta yi da jarumin, sai ku latsa alamar lasifika da ke saman hotansa don sauraro.
Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Adam A. Zango, ya ce babban burinsa shi ne ya kware wajen magana da harshen Turanci.
Zango, wanda aka haifa a garin Zangon Kataf na jihar Kaduna, ya yi karatun sakandare a birnin Jos na jihar Plateau ne.
Jarumin ya ce zai bar sana’arsa nan da dan wani lokaci domin ya je ya ci gaba da karatun boko.
A yanzu haka dai jarumin ya dauki malamin da yake ba shi darussa a gida, kafin ya koma makaranta don ci gaba da karatun.
“Yanzu haka na kammala sakandare kuma ina son ci gaba da karatu, ko da zuwa matakin difiloma ne. Abin da nake so shi ne na iya Turanci sosai,” in ji Adam Zango a wata hira da ya yi da BBC.
Sai dai wani abu da Adam ya ce yana ci masa tuwo a kwarya shi ne yadda wasu ‘yan boko suke masa kallon jahili duk kuwa da cewa “na yi karatun bokon sannan kuma ina da ilimin addini.”
Batun ilimin boko ne dai ya taba sa Adam ya wallafa wani habaici a shafinsa na Instagram da bai yi wa wasu ‘yan boko dadi ba, al’amarin da har ya sanya jarumin yin da-na-sani.
Waiwaye

Adam Zango FacebookHakkin mallakar hotoADAM ZANGO FACEBOOK
Image captionGwaska ne fim din da Adamu ya ce ya fi kawo masa kudi

Jarumin na Kannywood wanda har ila yau yana shirya fina-finai sannan yana rera waka, ya ce “na fara harkokin fim ne a Kano inda nake share-share da goge-goge a masana’antar kade-kade da ake kira ‘Landscope Studio’.”
Game da abin da ya sa ya shiga harkar fina-finai, Adam ya ce, “tsoron kada na zama dan jagaliyar siyasa ko kuma dan shaye-shaye ne ya sa na tsunduma harkar.”
Adam, wanda ake yi wa lakabi da ‘Usher’ wata inkiya da ta samo asali tun yana makarantar sakandare saboda iya rawa, ya fito a fina-finai fiye da 100, a inda kuma ya shirya wasu fiye da 20.
A fagen waka kuwa, jarumin yana da kundi guda shida kuma kowane kundi na dauke da wakoki 12, a inda wakarsa mai taken Gumbar Dutse ta zama bakandamiyarsa.
Adamu kamar yadda har ila yau wasu suke kiransa, ya ce a duk fina-finansa, ya fi son Ahlil Kitab saboda irin gudunmawar da ya bai wa addinin Musulunci a cikinsa, kamar yadda ya bayyana.
Sai dai kuma fim din da ya yi mai taken Gwaskane ya fi kowanne kwao masa kudi, duk da cewa shi ma fim din ya ci fiye da naira miliyan bakwai kafin a kammala shi.
Ni ba dan luwadi ba ne
Fitaccen jarumin ya ce a kullum yana kwana yana tashi da bakin cikin zargin da wasu suke yi masa na zama dan luwadi (neman maza).
Wannan ne ya sa a wani lokaci a baya jarumin ya dauki Alkur’ani ya rantse cewa bai taba neman wani namiji da lalata ba.
“Wannan abin yana hana ni barci, kai har ma na taba zuwa neman aure amma aka hana ni saboda haka,” in ji Zango.

Adam ZangoHakkin mallakar hotoADAM ZANGO FACEBOOK
Image caption‘Ba girman kai ne da ni ba, masoyana ne su kai yawan da ba zan iya bai wa kowa kulawar da yake so ba’

Game da batun cewa dan wasan yana da girman kai, jarumin ya kare kansa “Idan kana maganar masoya kana maganar miliyoyin mutane, to ta ya ya zan gamsar da su?”
Daga nan ya nemi masoyansa su rika yi masa uzuri domin shi ma mutum ne kamar kowa, kamar yadda ya ce.
A karshe ya yi magana kan yadda ake cewa ‘yan wasan Hausa “kudi suke nema kawai”, inda ya ce “muna yin fina-finan da za su kawo mana kudi.
Sources :bbchausa.com
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA