Kannywood
Wata Matashiyar Budurwa Tace Iya Halaka Kanta Akan Son Rahama Sadau
Shan koko kwanciyar rai, inji bahaushe, kuma dama ai so hana ganin laifi. Irin haka ne ta faru da wata budurwa mai suna Hidayah, wanda aka tabbatar da tsananin soyayyar da take yi ma Rahama Sadau.
Wani ma’abocin shafin Twitter Ali Basketball ne ya bayyana labarin wannan kyakkuawar budurwa mai kaunar fitacciyar jarumar Fim din Hausa, Rahama Sadau, inda yace a iya saninsa, yarinyar zata iya kashe kanta.
Ali ya rubuta a shafin nasa na Twitter cewa “@Rahama¬_sadau, wannan yarinyar zata iya kashe kanta, yar gani gashe nin ki ce”
Daily Trust ta ruwaito wani ma’abocin Twitter na daban shi kuma ya bayyana asalin sunan wannan yarinyar, inda ya bayyana sunan a matsayin Hidayah.
Daga karshe itama Rahama Sadau ta amsa wannan sako, inda tayi godiya kuma ta nuna kaunarta ga yarinyar, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com