Uncategorized

Wannan Nasiha ta Dr. Tilde Gaskiya ce Dokin Karfe:’Buhari Tunanin Bauta Masa Bai Kamata Ba

Wannan Nasiha ta Dr. Tilde Gaskiya ce Dokin Karfe:

“Buhari: Tunanin Bauta Masa Bai Kamata Ba”

Jiya da dare na karanta wani post na jumla daya a Facebook mai jan bango inda marubucin yake cewa cikin Turanci:

“In da akwai abin bauta da Allah ya yarda a bautawa banda Shi da na bauta wa PMB.”

Har da safe ina tunanin wannan post din wanda a ganina wuce gona da iri ne da bai kamata ba.

Hakika soyayya irin wannan za ta kai ga halaka kuma ta halaka wasu a baya. Soyayya mai tsanani ce ta kai ga bautar Annabi Isa, AS.

Soyayya ta rashin ganin laifi ko kuskure ko gazawa ko tsammanin iyawa da waraka daga wani mutum da jefa shi cikin hurumin bauta duk an yi hani da su a cikin Al-kur’ani mai-girma.

Hakika wannan bawan Allah da masu tunani irin nasa da Buhari zai ji su da ya yi tir da lamarinsu. Suna dora masa nauyin wata irin soyayya da ba zai iya dauka ba. Idan ya gaza kuma kan su ya kulle su shiga damuwa.

Duk dan’adam ba abin bauta ba ne ko da kuwa a tunani ba a zahiri ba, kowaye shi kuma komi martabarsa ko mukaminsa. Kalmar ‘bawa’ shi ne mafificin kirari da Allah yake wa manzonsa SAW wanda ya fi kowa da komi daraja wajensa.

Allah ya sani Buhari ya barranta da irin wannan soyayyar kamar yadda Annabi Isa ya barranta da mummunar soyayya da ake masa, wacce Allah ya kira bauta. Ni shaida ne a kan wannan.

Wasu daga Bauchi sun taba kai sarata wajensa da karyar wai na ce Buhari ba annabi ba ne. A gaba na da wani ya tado da zancen a 2010, Buhari ya ce: “Dr. Tilde ya yi gaskiya. Buhari ba annabi ba ne.” Su Yahaya Magayaki da sauran tawagar da muka ziyarce shi a lokacin su ne shaida.

Ita shuhura (fame) a kowace dai’rar rayuwa – walau ta addini, ko shugabanci, ko fim, ko adabi, dss – tana haddasa soyayya wacce wanda ake yiwa dole ya yi taka-tsantsan da ita don in ba haka ba za ta kai shi ga halaka ta hanyar jefa masa wahami game da shi kansa har ya kai ga zalunci, da tunanin komi zai iya, ko duk abinda ya yi daidai ne. Daga nan sai dagawa da take hakkin mutane. Mun ga wannan a shugabanni irinsu Stalin, da Hitler da Ahmed Sekou Toure da suka kashe mutanensu bila adadin. Ba ma fata mu ga irin wannan a Nijeriya.

Sau da yawa na ji mutane na cewa Allah ya taimaki al’ummarmu da Buhari ya zama Shugaban Kasa kuma ya nuna gazawarsa a fannoni dabam dabam. Suna cewa wannan ni’ima ce sosai. Ba don haka ba, da zai bar duniya ya bar mu da rikicin wasu da za su rika mai da shi gunki abin bauta.

Wannan almajirin ya yi gaskiya da ya ce:

Ta ya zan bidar wanda ba ya iyawa
Da zai mutu sannan ya zam ya ruba

Na bar wanga Sarki da zan so ya ce
A ranar tsayawa, “Ali, marhaba”.

Abinda Buhari yake bukata yanzu ba soyayya ba ne irin wannan. Addu’a yake bukata ta Allah – wanda shi kadai ya cancanci bauta a zahiri da badini – ya ba shi cikakkiyar lafiya, ya wala cikin iyalinsa, ya ci, ya sha, ya yi rahar nan tasa, kuma ya yi shugabanci nagari. Addu’armu ke nan gare shi da dukkan marasa lafiya, muna fata Allah ya amsa mana.

Dr. Aliyu U. Tilde
13 July, 2017″

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button