Kannywood

Kannywood Zata Saki Fim Dinta Mai Kama Da Boko Haram A Kasar Ghana – Abu Hassan


Shahararren dan wasan fina-finan Hausa Kuma wanda ya shirya fim din Abu Hassan ya ce zai fara nuna fim din ne a kasar Ghana kafin yayi a Najeriya.

Zaharaddeen ya fadi haka ne a wata hira da ya yi da Mohammed Lere a garin Kaduna.

Zaharaddeen ya ce ya yanke shawarar fara nuna fim dinne a kasar Ghana ganin cewa su da wadansu jarumai mata da ya hada da Halima Ateteh da Jamila Nagudu za su ziyarci kasar Ghana domin yin shagulgular Sallah Karama.

” Muna da Masoya masu dimbin yawa a kasar Ghana saboda haka abinda zan yi zai yi musu dadin gaske. Bayan haka kila in nuna shi a kasar Nijar kafin in dawo Najeriya.
” kasan yanzu mun dakatar da fitar da fim ta hanyar ‘yan kasuwa saboda hasara da muke yi ga masu yi mana fasakwaurin fim din. Za ka ga tun kafin ka gama natsuwa sun buga tasu suna ta siyarwa a kasuwannin kasar nan.
 Zaka ga ana ta turawa har ta waya. Hakan sai kaga ya sa furodusa ya tafka hasarar gaske.”

” Yanzu duk fim idan ya fito a gidan kallo zamu fara saka shi kafin nan ya shigo kasuwa. Hakan zai sa a rage hasara sosai.

Da muka tambayeshi game da jihohin da basu da gidajen kallo irin wadanda ake dasu a Kano Zaharaddeen ya ce ” Lallai masu ruwa da tsaki a harkar shirya fina-finan sun kula da haka kuma suna shirin fitar da hanyoyin da za a cike wannan gibi.

©hausatop

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA