Uncategorized

Jikanyar Sarkin Musulmi Muhammadu Tambari Ta Yi Zarra A Karatun Digir-Digir Akan Injiniyanci Na Jami’ar Leeds Dake Ingila!


Dr Zainab Adiya ta Kammala digirin digirgir na sanin makamar Injiniyanci na Sinadarai a daya daga cikin manyan Jami’oi duniya masu girma ta Leeds dake garin Landan a Ingila. 

Dr Zainab Adiya ta kasance daga cikin mata yan Najeriya wadda kuma jikanyar Sarkin Musulmi Muhammadu Tambari. 
Dr Zainab Ibrahim Sarkin Gobir Adiya ta zama cikin jerin dalibai wadanan jami’ar Leeds dake Ingila ta girmamma saboda kwazo da binciken ta,  tana cikin wadanda suka samu karbar shaidar kammala digir digir na zama Dakta a fannin Ilmin injiniyancin sinadarai.

Dr Zainab Adiya ta kasance cikin yan Afrika kalilan da suka yi fice a wannan karni a fannin binciken nazarin Sinadarai, samar da iskan masana’antu da hada wasu Sinadarai na hasken rana tare da iska a jami’ar Leeds. 

Ta rubuta kasidodi na bincike har guda biyu da aka buga a wasu mujjalun duniya masu girma da kima akan lamarin sinadarai dabam dabam da ake kira iskan ‘Hydrogen Energy’.

Haka ma yanzu haka tana akan wallafa wasu kasidu akan bincike da tayi na wasu fannoni biyu na inganta samar da sinadarai na oxygen a jami’ar Leeds dake Ingila. 

Dr Zainab Adiya wadda take jikanyar Sarkin Musulmi Muhammadu Tambari ce daga jinin Sarkin Gobir Adiya, tana da kujerar din din a kwamitin mussaman na zabe Kungiyar Dalibai yan Najeriya dake kasar Ingila baya ga kasancewa wakiliyar yankin Afrika a sha’anin inganta karatu da bincike na jami’ar Leeds. 

Haka ma Dr Zainab Adiya tana da kujera Cibiyar Inganta Sinadarai ta Amurka (AICHE) da takwararta ta Ingila mai kula da samar da bincike inganta Sinadarai da makamashi ta Ingila (ICHEME)  DA cibiyar nazarin sinadarai masu amfani ga hasken rana da bunkasa iskan masana’antu ta Ingila mai suna (UKCCS).

Mahaifinta Alhaji Ibrahim Sarkin Gobir Adiya wanda jinin Sarkin Gobir Adiya daga zuri’ar Sarkin Musulmi Tambari ne tare da sauran yan uwa da abokan arziki suka shaidi bikin karbar kyaututtuka da saukar karatun na Dr Zainab Ibrahim Adiya a garin Landan dake Ingila a makon da ya gabata.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button