Hazikin Yaro Mahaddacin Kur’ani Na Bukatar Agajin Gaggawa
Labarin Idris Bello Umar Ingawa, Yaro dan kimanin shekaru 13 wanda ya haddace Alkur’ani mai girma kuma Jjka a wajen Babban Limamin Ingawa.
Idris Bello Umar Ingawa, yaro ne dan kimanin shekaru 13, kuma yaro ne mai hazaka a makaranta wanda tun yana dan kimanin shekaru 12 ya haddace alkur’ani mai girma. Sannan kuma jikane a wajen babban limamin ingawa dake jihar katsina.
Wata rana ya dawo daga makaranta saiya fadi. Faduwar keda wuya sai kashin cinyarsa ya tsage daga nan sai wani nama ya fito a cikin cinyar. Daganan cinyar ta rinka zubar da ruwa mai yawan gaske, wanda hakan ya haifar masa da rashin bacci da rashin nutsuwa, yakan kwana yana kuka saboda zafi da radadin da ciwon ke masa a kafarsa.
Hakika Iyayen wannan hazikin yaro sun yi ta dawainiya da shi zuwa asibitoci daban daban domin nemar masa lafiya, ciki har da asibitin birnin Katsina, Kankiya, Daura da Ingawa, amma har yanzu abin ya ci tura.
Wannan dalilin ne ya sa yanzu aka maido da shi jihar Kano domin duba lafiyarsa. Inda yanzu yana wajen kakarsa, a unguwar gobirawa dake karamar hukumar Dala. Kuma suna zaune ne a gida saboda rashin kudin da za a yi masa aiki a Asibiti.
Duk da wannan rashin lafiya da yake, da zubar da ruwa da cinyarsa take, a hakan idan ka je za ka ga yaron gwanin sha’awa cikin kamala illa kwalla da suke zuba daga idansa yana rike da charbi yana lazimi gwanin ban sha’awa.
Hakan ta sa wakilin Jaridar RARIYA ziyartar gidan da yake, bayan duba yaron iyayen yaron sun miko kokon bara domin sanar da bayin Allah ko za’a dace a samu wanda za su taimaki wannan hazikin yaro.
Yanzu ana bukatar a kalla dubu dari uku (#300, 000) domin yi masa aiki. Jama’a a taimaka mai taro da sisi, domin ceto rayuwar wannan yaro.
Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Duk wanda ya kawar wa mumini wata masifa daga cikin masifun duniya, to shima Allah Zai kawar masa wata masifar daga cikin masifun lahira, Kuma duk wanda ya rufa wa wani musulmi asiri, to shi ma Allah zai rufa masa asiri a Duniya da Lahira. Allah Yana taimakon bawa, matukar bawan bai gushe ba yana taimakawa Dan’ uwansa”.
Za ku iya tuntubar wakilinmu dake jihar Kano, Bashir El-Bash a wannan lamba 08036275108.
Ga masu son taimakawa kuma ga
Account Number: 5191041998,
Bank EcoBank,
Name: Abdullahi Bashir
Duk wanda ya taimaki wani, Allah zai taimaka masa.