Adam Zango Yasa Gasa Mai Tsoka Akan Film Din Gwaska Returns
Fitaccen jarumin nan na Kannywood Adam A Zango ya sanya gasa akan film din nan na gwaska returns wacce ke dauke da kyauta mai tsoka ga duk wadanda sukayi nasara.
Gasar dai kaso biyu ce; wato gasar maza da kuma ta mata.
Maza zasu kirkiri rawa akan kida na wakar da zasu yi a cikin film din gwaska returns.
Wadanda suka yi nasarar zuwa na daya wajen bin kidan da wakar yadda ya kamata to za’a basu kyautar naira dubu dari da hamsin, da T-shirt ta gwaska da hula.
Wadanda suka zo na biyu za’a basu kyautar naira dubu dari da T-shirts da hula.
Na uku kuma za’a basu Naira dubu hamsin. Sannan kuma su zasu hau wakar a cikin film din na gwaska returns.
Mutum 3 zuwa 5 zasu iya haduwa su hau wakar a wannan gasa.
Mata kuma anaso suyi miming na wakar cikin shauki na soyayya, amma fa mace daya ake son gani a duk video.
Duk wacce tazo ta 1 tanada kyautar waya da kuma atamfa 3, material 3 da kuma gyale 3.
Ta 2 kuma tanada kyautar karamar waya da kuma kuma atamfa 2, material 2 da kuma gyale 2.
Ta uku kuma tanada kyautar kuma atamfa 1, material 1 da kuma gyale 1.
Za’a fara gasar ne yau (5th July 2017) zuwa sati biyu.
Yadda gasar take shine zaku dauki video na rawar taku sannan sai kuyi posting a page dinku na Instagram sai ku rubuta haka a caption dinku.
#gwaskareturncompetition
ko kuma Ku turo ta WhatsApp a layin wayar wannan gasa kamar haka:
WhatsApp__+2348032863252
ALLAH YA BAIWA MAI RABO SA’A!!
Daga prince Zango production Nigeria Limited..
sources:arewamobile.com