Kannywood

Zan Bawa Masoyana Masoyana Mamaki Inji Rahama Sadau

Advertisment

Bayan hutu da aka sha na rashin fitar finafinan Hausa a kasuwa, masu shirya finafinan Kannywood sun kammala shiri tsaf domin sakin wasu daga cikin manyan finafinai da ake ta yi musu jiran tsammani tsawon lokaci.
A cikin finafinan da za ta saki sun hada da fim din da shaharariyar jarumar nan watau Rahama Sadau, wanda kusan za a iya cewa, shi ne fim na farko da zai fita kasuwa karkashin kamfaninta Sadau Pictures.
Wannan shahararren fim da aka dade ana jira ‘RARIYA’ ya samu karbuwa matuka tun kafin ya fita, wanda yanzu aka tabbatar da cewar za a fara haska a manyan sinimun kasar nan ranar 26 ga watan Yuni, 2017, watau ranar Sallah kenan.
Tun a baya, a ci gaba da kokarin da yake na tallata sabon fim dinsa mai suna Rariya, kamfanin SadauPictures ya sanya gasar rawa ga ma’abota kallon finafinan Hausa, inda za a lashe kyautuka masu gwabi ga dukkan wadanda suka sami nasarar lashe gasar.
Kamar yadda suka sanya a shafukansu na sada zumunta: Twitter, Facebook da Instagram, SadauPictures sun bayyana cewar gasar ta rawa ce kadai, wadda ake son a kunna wakar fim din mai take ‘Tankade na yo na sa Rariya’ sannan a taka rawa wadda ta fi ta jaruman ciki.
Tuni dai matasa suka fara gudanar da wannan gasa a shafukan Instagram, inda suke taka rawa sannan su dora, yayin da su kuma kamfanin SadauPictures za su sake sakawa a shafukansu.
Wannan dai shi ne karo na farko a tarihin masana’antar shirya finafinan Hausa da wani kamfani ya bugi kirji tare da sanya gasa makamanciyar irin wannan. Wadda za a ci kyautuka da suka da: Talabijin, Kayan Sauti da kuma Fanka.
Shugabar kamfanin, jaruma Rahma Sadau ta bayyana a shafinta na Instagran cewar gasar ta kowa da kowa ce, kuma za a gabatar da wadanda suka yi nasara a gidan talabijin na Arewa24 karshen watan nan da muke ciki.
Yau dai kimanin mako uku kenan ana fafatawa a wannan gasa, inda kowa yake kokarin ganin ya zamo zakaran gwajin dafin da zai lashe, sannan ya samu ganawa da Rahma Sadau.
Fim din Rariya, na daga cikin finafinan da masoya kallon finafinai ke matukar tsumayi a halin yanzu, domin ya hada jarumai irin su Ali Nuhu, Rahma Sadau, Sadik Sani Sadikm Fati Washa, Hafsat Idris da sauran su. Babban darakta Yaseen Auwal ne ya bada umarni.
Babban abin da masoya wannan jaruma ke son ji yanzu shi ne, lokacin da za a saki fim din, domin sun yi tanadin yin fitar dango domin su kashe kwarkwatar da ta dade tana yawo cikin idon su.
Ga dukkan alamu za a iya cewa wannan shi ne karo na farko wani fim din Hausa ya samu tagomashi a Nijeriya, domin za a haska shi a sinimu irin na zama a garuruwan Kano, Kaduna, Abuja da kuma Ibadan.
Jarumar ya bayyana ranakun da za a saki fim din yayin tattaunawar musamman da wakilinmu ta wayar tarho, inda ya ce duba da yanayin irin aikin da aka yi wa fim din, kamfanin Sadau Pictures sun yanke shawarar sakinsa a bukukuwan sallah.
“Rariya fim ne da aka kashe makudan kudade wajen yin sa, saboda haka hanyoyin tallata shi kadai sun bambanta da yadda ake yi wa sauran finafinai. Mun zabi lokacin bukukuwan karamar sallah ne domin domin bawa mutane damar kallon sa kasnacewar ana hutu.” A cewar Rahama Sadau

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button